Gwamnatin Ado Tambai Tana Samar Da Ci Gaba A Dawakin Tofa – Inji Abdallah Bataye

0
407

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

MATAIMAKI na musamman ga Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Kan kafar sadarwa ta zamani Malam Abdallah Ishaq Bataye ya ce Shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya samar da ci gaba mai kyau a fadin yankin.

Ya sanar da hakan ne a zantawar sa da wakilin mu a Dawakin Tofa, inda ya jaddada cewa yanzu Karamar hukumar Dawakin Tofa ta bunkasa ta kowane fanni duba da yadda kowane sashe yake rabauta da aiyukan alheri ba tare da nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi ba.

Abdallah Bataye ya Kara da cewa al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa sun dace da jagora Wanda Kuma yake gudanar da aiyukan sa bisa la’akari da bukatun al’ummar kowane bangare na mazabu 11 dake Karamar hukumar wanda hakan abin a yaba ne.

Ya ce “an sami ci gaba mai albarka a fannin ilimi da kula da lafiya da tsaro da aikin gona da Kuma baiwa Mata da matasa horo da jarin sana’oi domin bunkasa dogaro dakai da Kuma gudanar da manyan aiyukan raya kasa kamar dai yadda ake gani a kowace mazaba.

Haka kuma Bataye ya sanar da cewa a fannin ilimi da tsaro, an yi abubuwa muhimmai wadanda lokaci bazai bari a fayyace su duka ba sannan kowa yana ganin yadda al’amura suke tafiya cikin nasara a dukkanin mazabun da ake dasu guda 11 dake fadin yankin.

Abdallah Bataye ya yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da yake yi wajen kawo managarcin ci gaba a Jihar Kano duk da irin kalubalen tattalin arziki da ake fama dashi a duniya baki daya, inda Kuma ya yi fatan cewa za a ci gaba da samun zaman lafiya da karuwar arziki a Jihar Kano da kasa baki daya.

A karshe, ya sha alwashin fara bayyana cikakkun bayanai kan aiyukan alheri da majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa ta gudanar da Kuma wadanda take gabatarwa bisa jagorancin Alhaji Ado Tambai Kwa ta yadda al’umma zasu Kara fahimtar irin ci gaban da Karamar hukumar ke samu batare da tsaiko ba.

Leave a Reply