APC A Jihar Kano Tana Kara Karfi – Inji Ado Tambai

0
351

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya bayyana cewa Jam’iyyar APC tana cikin yanayi mai kyau a Jihar kano bisa yadda Gwamna Dokta Abdullah Umar Ganduje ya ke kokari wajen bunkasa Jihar.

Ado Tambai kwa ya yi wannan tsokaci ne a ganawar su da wakilinmu, inda ya sanar da cewa Jam’iyyar APC a Jihar kano tana kara karfi da bunkasa duba da yadda Gwamna Ganduje da dukkanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar suka hada hannu wajen kawo ci gaba mai kyau gare ta kuma a matakai daban – daban.

Ya ce suna gamsuwa da yadda Jam’iyyar ta APC ta ke kara samun nasara wajen gudanar da aiyukan alheri ga al’ummar Jihar kano bisa la’akari da bukatun kowane bangare, wanda hakan ya nunar da cewa da yardar Allah APC za ta lashe zabukan shekara ta 2023 da gagarumin rinjaye.

Alhaji Ado Tambai kwa ya godewa Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnatin sa saboda namijin kokarin da suke yi wajen inganta raguwar al’umma da samar da aiyukan raya kasa a Birni da kuma yankunan karkara bisa tsari da sanin ya kamata ta yadda kowa zai amfana da romon dimokuradiyya mai kyau.

Shugaban karamar hukumar ta Dawakin Tofa, ya yi amfani da wannan dama wajen taya shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas murnar kaddamar da shi da aka yi a matsayin halastaccen shugaban Jam’iyyar a Jihar kano, tare da Jaddada cewa zasu ci gaba da gudanar da aiyukan alheri ga al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa domin samar da ingantaccen ci gaba a fadin yankin.

Leave a Reply