An kwashe sojojin dake tsaro a Kuje, sa’o’i 24 kafin Kai hari magarƙama

0
345

Wata majiya me ƙarfi ta sanarwa manema labarai cewa, tun gabanin harin, anriga da an kwashe sojojin dake kewayen kuje kusan sa’o’i 24 gabanin kai hari magarƙamar kujen, Abuja.

A ranar Laraba, Wasu majiyoyin tsaro suka bayyana haƙiƙanin abinda ya faru, suna cewa sojojin da aka tura yankin basu gama sanin gurinba, wadanda suka yi ma yankin farin sani kuma, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 da suka wuce kafin yan ta’adda sukai hari gidan yarin.

Majiyar tayi mamakin dalilin da yasa aka kwashe su jamian da suka san yankin sa’o’i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samu wasu da suka maye gurbin su ba, har yan ta’addan suka far ma Yankin, inji Vanguard.

Leave a Reply