Gani ga Wane
Sri Lanka: Masu zanga-zanga sun mamaye fada har sai shugabanni sun sauka
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657494981481.jpg)
Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a Colombo a ranar Asabar inda suka buƙaci ya yi murabus bayan shafe watanni ana zanga-zangar.
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657494997963-768x1024.jpg)
Masu zanga-zangar sun ce za su ci gaba da mamaye gidajen shugaban ƙasa da na firaministan ƙasar Sri Lanka, har sai shugabannin biyu sun yi murabus a hukumance. Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya ce zai sauka daga mulki ranar 13 ga watan Yuli, kamar yadda kakakin majalisar ya bayyana a ranar Asabar.
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657494986961.jpg)
Ana dai zargin shugaban kasar ne da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, wanda ya janyo karancin abinci da man fetur da kuma magunguna tsawon watanni.
Sai dai ba a ga shugaban ko kuma waninsa ya yi wata sanarwa da kansa ba. Wasu majiyoyin soji sun shaida wa BBC cewa a halin yanzu yana cikin wani jirgin ruwan sojin ruwa a ruwan kasar Sri Lanka. Majiyoyin sun ce dan uwansa, tsohon Firayim Minista Mahinda Rajapaksa, yana sansanin sojin ruwa a ƙasar.
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2022/07/FB_IMG_1657494977508.jpg)
Shi ma Firayim Minista na yanzu Ranil Wickremesinghe ya ce zai sauka daga mukaminsa biyo bayan zanga-zangar da aka yi ranar Asabar, inda aka ƙona gidansa na ƙashin kansa. Sai dai masu zanga-zangar na ci gaba da nuna shakku kan manufar shugabannin.
Al'ajabi
Yadda aka horar da ɓeraye wajen ceto mutane yayin girgizar ƙasa
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/02/07-90847351-sar-rats.jpg)
Kampanin Apopo na ƙasar Belgium ya horar da wasu haziƙan ɓeraye domin yin aikin ceto ga waɗanda ɓaraguzan girgizar ƙasa suka danne har yau ba a gano su ba.
“Anyi amfani da ɓeraye ne saboda a yanayin tsarin halittar su, suna da sha’awar sanin abu, da kuma son kutsa kai da bincike, wannan dalili yasa aka gane tsaf zasu iya taimakawa wajen ceto,” in ji Donna Kean, ƙwararren masanin kimiyyar ɗabi’a kuma shugaba mai jagorarantar aikin.
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/02/09-90847351-sar-rats.jpg)
“Banda ɗabi’ar ɓera na binkice da shige shige, ƙanƙantar halittar su, da baiwar jin ƙamshin da wari koda daga nesa, ya beraye suka zama mafi chanchanta don yiwa duniya wannan aiki”, in ji Kean.
KU KUMA KARANTA: Allah ɗaya gari bam bam! Gizo-Gizo, abincin yau da kullum a Kambodiya
An sanyawa ɓerayen wata babbar jaka da take ɗauke da na’urar GPS ta zamani da kyamarar ɗaukar hoto mai inganci, da kuma makirufon.
Haka kuma akwai wata na’urar wayar salula da za a iya magana da mutanen da suka maƙale amma ba su kai ga rasa rayukansu ba.
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/02/01-90847351-sar-rats.jpg)
Sannan za a iya ganin mutumin da abin ya rutsa da shi, gami da gane irin yanayin da yake ciki, sannan a gano hanya mafi sauƙi da za a iya ceto shi a fito da shi.
Wannan ya zama izina garemu mutane, idan har ɓera yana kishin ƙasarsa, yana bada gudunmawa mai mahimmanci wajen cigaban ƙasa, ya kamata mu tambayi kanmu, mu wane gudunmawa muke bawa ƙasar mu domin cigaban ta, a matsayin mu na yan Adam.
Gani ga Wane
Kotu ta umurci budurwa ta biya saurayinta N150,000 bayan ta karɓi kuɗin mota N3000 ta kuma ƙi amsa gayyatarsa
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/01/642d6b3b7accfa1f.jpg)
Kotu ta umarci wata mata da ta karɓi naira dubu uku kuɗin mota wajen saurayinta domim ta ziyarce shi, amma daga baya ta kashe wayarta, ta ƙi zuwa, da ta biya saurayin kuɗi naira dubu N150,000, bayan da saurayin ya kai ƙarar budurwa tasa kotun.
Kotun da ke zama a jihar Enugu ta yanke hukuncin ne dan koya wa mata masu yaudara darasi, domin shari’ar ta zamo izina ga wasu matan.
KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum shaƙe budurwarsa saboda cin amana, ya kuma cinna wa kansu wuta
Wani Lauyan Najeriya mai suna @Egi_nupe_ a shafinsa na tweeter, ya bayyana hakan a shafin Twitter, ya ce matar ta kashe wayarta bayan ta karɓi kuɗin kuma hakan ya fusata saurayin nata.
Mutumin da bai ji daɗin abin da ya faru ba, ya garzaya kotun shari’ar Enugu inda ya yi nasara.
A cikin hukuncin, alkalin kotun ya ce abin da matar ta aikata yaudara ne.
Adadin tarar da aka ɗora wa matar, an yi ne don ya zama izina ga sauran mata masu irin wannan dabi’a ko tsare-tsare na yaudara.
'Yansanda
Yadda aka tsinci gawar ma’aurta a kan gadon aurensu a Kano
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/01/images-4.jpeg)
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne aka tsinci gawar wani magidanci mai suna Sulaiman Idris mai shekaru 28 tare da gawar matarsa Maimuna Halliru mai shekaru 20 a kan gadon aurensu.
A wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce ma’auratan ba su fito daga gidansu ba, tun ranar Laraba 02/01/2023, inda suka shafe kimanin awa 23 a ɗaki.
Ya ce “A ranar Litinin, 03/01/2023 da misalin ƙarfe tara na safe, an samu rahoto daga ƙauyen Kwa, na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, a jihar Kano cewa wasu ma’aurata, Sulaiman Idris, da matarsa Maimuna Halliru, ba su fito daga gidansu ba tun ranar 02/01/2023 da misalin ƙarfe 11:00 na dare.
Binciken farko, an gano cewa ma’auratan da suka mutu sun kunna wuta don dumama ɗakinsu saboda sanyin da su ke ji, kuma ko’ina a kulle, dalilin haka hayaƙi ya balbale su a lokacin da suke barci.
“Lokacin da kakar mijin buɗe ƙofar ɗakinsu da ƙarfi, sai ta tarar da ma’auratan basa motsi a kan gadon su, ta kuma iske da ragowar hayaƙi a ɗakin.
“Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya umurci tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Ahmed Hamza,DPO na ‘yan sandan reshen Dawakin Tofa da suje suga wurin, inda suka ka kai ma’auratan asibitin ƙwararru na Murtala Mohammed da ke Kano kuma a nan wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci al’ummar jihar Kano da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da wuta, da kuma lantarki, sannan a kula da ɗaukar matakan kariya saboda lokacin sanyi yana da alaƙa da haɗarin gobara.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai10 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano
Pingback: Shugaban Sri Lanka ya yi murabus ta hanyar wasiƙa bayan ya gudu zuwa Singapore | Neptune Prime Hausa
Pingback: Ƙasar Sri Lanka ta zaɓi sabon shugaban ƙasa | Neptune Prime Hausa