An kama waɗanda suka ƙona gawar tsoho ɗan shekara 90, suka kuma sace masa N430,000.00

0
370

Jami’an ‘yan sanda a jihar Sokoto sun yi nasarar cafke wasu miyagun mutane 6 da ake zargi da kasancewa mambobin haramtacciyar kungiyar ‘yan banga da ake kira ‘Yan Sakai a jihar. A cewar gidan talabijin na TVC, an kama wadanda ake zargin ne da laifin kashewa da kuma ajiye gawar wani mutum mai shekaru 90 da haihuwa.

Gidan talabijin na TVC ya kuma ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Zangon Atti da ke Ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar.

An ce waɗanda ake zargin sun kama marigayi Muhammad Riskuwa tare da ɗansa Shehu Mamman bayan tattaunawa da su, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya harbe marigayin har lahira. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sanusi Abubakar ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun kuma amsa cewa sun dira gidan mamacin tare da kwace kudi N430,000.00 bayan sun ƙona gawar sa.

Sanusi Abubakar ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply