Muna kan bincike, amma bamu tabbatar da Jami’inmu ne yayi wannan Barnaba – KAROTA

0
228

Daga Shafa’atu Dauda, Kano

Bayan wani jami’in KAROTA ya cakawa wani matashi wuƙa a gefan klƙirjinsa, yanzu haka hukumar ta ce tana kan bincike akan lamarin.

Da yake zantawa da Jaridar Neptune prime a daran jiya Juma’a, kakakin hukumar Nabulisi Abubakar kofar Na’isa ya ce, “Mun san da faruwar wannan abu, wanda haryanzu muna kan bincike domin ba iya yan KAROTA ne a wajan ba.

“Tafiyar haɗin gwiwar ne da jami’an mu dana Civil defence dana police tare yan Bijilanti aka yi wannan aiki na hawan Salla a Dorayi.

“Dan haka dole sai mun tattara rahotanni daga ɓangarori kafin mu fitar da sakamako akan wannan abu, kuma indai har muka kama jami’in mu da laifi to za’a dau mataki akansa.

“Kazalika mukanmu akwai wasu cikin jami’an mu da aka jiwa raunuka harma da ‘yan sanda, wanda duk za’abi abun a hankali wajan warware komai da gano inda matsalar take.”

Nabulisi ya ƙara da cewa, “babu wani da ya tabbatar musu da cewa jami’in su ne yayi wannan ɓarna, amma bazai tabbatar ba tunda baya wajan sai abun da bincike ya gano akai.”

Tun a ranar uku ga salla ne da Sarkin Kano yayi hawan Salla na Dorayi, inda aka sami wani jami’i ya cakawa wani matashi mai suna Riduyyudeen makami a jiki.

Yayan matashin, Fakaruddeen ya tabbatarwa da Jaridar Neptune prime cewa yanzu haka an kwantar da ƙanin nasa a asibitin Aminu Kano wanda yake cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply