An Kama Matar Da Ta Yi Yunkurin Sayar Da Dan Kishiyarta

0
318

Daga Rabo Haladu 

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen JiharZamfara ta kama wata mata da take zargi da yunƙurin sayar da yaro ɗan shekara biyu.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Ayuba Elkana inda ya ce an kama matar ne tun a ranar 8 ga watan Janairu a yankin Tullukawa da ke Gusau inda ake zargin matar da yunƙurin sayar da ɗan kishiyarta.

Matar wadda asalinta mutumiyar ƙauyen Danyade ce da ke Maradi a Jamhuriyyar Nijar, an kama ta ne ɗauke da ɗan kishiyarta wadda ta shaida wa jami’an tsaro cewa ta sato yaron ne daga kishiyarta domin ita ma ta rama sata da sayar da ɗanta da kishiyarta ta yi a baya.

Amma daga baya ta ƙara shaida wa jami’an tsaro cewa ta yi yunƙurin sayar da yaron ne domin samun kuɗin biyan buƙatunta na yau da kullum.

Rundunar ƴan sandan ta ce za a miƙa wadda ake zargi zuwa ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin zurfafa bincike.

Leave a Reply