Taron APC: An Gargadi Masu Kokarin Matsawa Masu Zaben Dan Takara Da Su Kiyaye Yin Hakan

0
349

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

KWAMITIN shirya zaben dan takarar da zai tsayawa Jam’iyyar APC takarar shugaban kasa a tarayyar Najeriya sun bayyana gargadi karara ga masu kokarin matsawa masu zaben dan takara su rubuta sunan da suke bukata sabanin irin tanaje tanajen yin zaben ya tanada.

A lokacin da aka fara gudanar da zaben dan takara da misalin bayan karfe daya na daren Laraba, sai yan kwamitin suka bayyana cewa akwai wasu da ke kokarin matsawa masu zaben sai sun zabe wani dan takarar da ba a son ran su ba.

“Mun samu labarin cewa akwai wasu da ke matsawa yan takara sai sun zabi wani dan takara, saboda haka duk wanda muka samu ya na matsawa wani ya zabi dan takara, to wannan mutui ya hanzarta kai kukansa ga kwamitin shirya zaben domin daukar matakan da suka dace”. 

Leave a Reply