Asiwaju Bola Tinubu Ne Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar APC Da Kuri’u 1271

1
340

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

JAM’IYYAR APC a tarayyar Najeriya ta bayyana sakamakon zaben da kowane dan takara ya samu daga cikin yan takara Goma 14 da suka tsaya neman Jam’iyyar ta tsayar da su takarar kujerar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar.

Kamar yadda aka sanar a filin wasa na Eagle Square a garin Abuja bayan kammala taron, an bayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin a Jam’iyyar ta APC.

Ga kuma yadda sakamakon zaben ta kasance:

Asiwaju Ahmad Bola Tinubu – 1271

Ahmad Lawal – 152

Rotimi Ameachi – 316

Gwamna Yahya Bello – 47

Farfesa Yemi Osinbajo – 235

Ahmad Rufa’I Sani Yarima – 4

Pastor Tunde Bakare – 0

Chukwumeka Nwajiba – 1

Engr David Omahy – 38

Sanata Farfesa Ben Ayade – 37

Sanata Rochas Okorocha – 0

T N Jackreach – 0

Dokta Christoper Onu – 1

Chief Eco Abalu Mukolu – 0

1 COMMENT

Leave a Reply