Yan Takara 14 Ne Za Su Fafata A Zaben Yan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC

0
324

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

JAGORORIN kwamitin shirya zaben yan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC domin tsayawa zaben takarar shekarar 2023 sun bayyana cewa ya zuwa yanzu, yan takara Goma sha hudu (14) ne za su fafata a zaben.

Bayan da aka samu yawan yan takara mutum Tara da suka bayyana janyewarsu, wasu suka bayyana goyon bayan su ga dan takara Bola Ahmad Tinubu inda wani daga cikin yan takarar ya bayyana goyon bayansa ga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Wannan janyewar ta biyo bayan damar da aka ba yan takarar ne su yi wa Jama’ar da suka halarci taron da kuma duniya bayani.

A cikinsu har da wata yar takara mace guda daya da ke takarar shugaban kasa inda ta bayyana cewa ta janye, kana ta bayyana goyon bayan ta ga dan takara Cif Bola Ahmed Tinubu, ta ce ta na matukar nuna kauna da Soyayya ga daukacin yan Najeriya.

Leave a Reply