An Ɗage Shari’ar Ɗan Sarauniya A Kano Saboda Dalilan Tsaro

0
494

Daga; Rabo Haladu.

AN ɗage shari’ar Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya zuwa Juma’a 4 ga watan Fabrairun 2022.

A cikin wata wasiƙa da Magatakardar Kotun Majistare da ke Nomansland da ke Kano Auwal Muhammad T/Wuzurci ya saka wa hannu, an ɗaga zaman ne saboda yanayi na staro.

Ya bayyana cewa a ranar 3 ga wata wadda ita ce asalin ranar da za a yi shari’ar Mu’azu Magaji, a ranar ne za a yi shari’ar Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara kuma jami’an da za su kai Sheikh Abduljabar kotun da ake masa shari’a a Upper Shari’a Court da ke Ƙofar Kudu su ne dai jami’an da za su kai Mu’azu Magaji kotun da za a yi masa shari’a a Nomansland.

Hakan ya sa aka ɗage shari’ar Dan Sarauniya zuwa 4 ga watan Fabrairu da misalin 2:30 na yamma.

A makon da ya gabata ne ‘yan sanda a Abuja, suka kama Mu’azu Magaji wanda shi ne tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano.

Sun kama shi ne bisa tuhume-tuhumen da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yake masa na ɓata masa suna da zaginsa da kuma zargin yin abubuwan da zai kawo taɓarɓarewar zaman lafiya.

Leave a Reply