Hukumar Kwastan Ta Kano/Jigawa Tana Hana ‘Yan Fasa kwauri Sakat

0
472

Daga; Rabo Haladu.

HUKUMAR Kwastan ta shiyar Kano/Jigawa ta hana ‘yan fasa kwaurinta yin barci don kuwa kodayaushe suka zo aiwatar da fasa kwaurinsu musamman ma na haramtacciyar shinkafa ta hanyar duk da suka sani ta babur ko mota da makamantansu sai kwatsam su ga jami’an kwastan tamkar an jefo su. Wannan ya fi faruwa a hanyar Kano zuwa Gumel da kan hanyar Danbatta da hanyar Kano zuwa Ringin.

Rahotan hakan ya same mu ne ta hanyar binciken da Editanmu, Malam Zubair Abdullahi Sada ya gudanar da gani da idonsa a yau Laraba, bayan ya soke labarin da ke kan wannan shafi da aka buga da safe, inda ya ce, ko shakka babu kafafen yada labarai na wannan zamani sai sun tashi tsaye don tantance labaransu, don kuwa labarin kwastan da aka dauka a wannan jarida Gaskiya Ta Fi Kwabo ya sami tangarda. Editan ya ce, wakilanmu yardaddunmu ne sai dai wani lokaci suna haduwa da kalubalen daidaiton labari, wannan ne ma ta sanya aka janye wancan labarin.

A cewar Editan GTK, an gano cewa mazauna kauyukan nan da garuruwan nan su ne suka lallaba suka yi hira da wakilinmu har suna cewa su ba su san an rufe boda ba domn shugaban Hukumar Kwastan mai kula da Kano/Jigawa kwanturola Suleiman Pai Umar tamkar bai san yankin ba kwata-kwata.

Editan namu ya yi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Kwastan na shiyar Kano/Jigawa Kwanturola Suleiman Pai Umar ta wayar tarho amma lambarsa ba ta shiga, kuma ofis din ma ayyuka sun yi yawa ba a sami damar hada su su tattauna ba, kila sai an sami saukin al’umma.

Leave a Reply