Connect with us

Kasuwanci

Akwai Ingantaccen Tsarin Tsaro A Kasuwar Duniya Ta Kaduna – Fatima

Published

on

Daga, IMRANA ABDULLAHI.

AN bayar da tabbacin samun ingantaccen tsarin kula da harkokin tsaron dukiya, lafiya da rayukan jama’a lokacin gudanar da cin kasuwar duniyar kasa da kasa da za a bude gobe Asabar a Kaduna.

Shugabar kwamitin yada labarai Hajiya Fatima Abdullahi da Kanar Jibril Hassan mai ritaya duk sun bayar da tabbacin samun ingantaccen tsarin tsaro a lokacin gudanar da kasuwar ta Bana da za a bude a gobe Asabar 26 ga watan Fabrairu 2022 zuwa ranar Lahadi 6 ga watan Maris 2022.

Kasuwar dai ta fara ne tun daga yau Juma’a 25 ga watan Fabrairu 2022, da ake saran dimbin jama’a daga ko’ina a fadin duniya za su halarta domin kawo kayayyakin amfanin al’umma daban daban.

Hajiya Fatima ta ci gaba da yin kira ga jama’a daga ko’ ina suke a fadin duniya da kowa yazo kansa tsaye ba tare da wata fargaba ba domin duk wani tsarin kula da lafiya, dukiyar al’umma a cikin da wajen wannan kasuwar duk an tanada, yadda aka fara gudanar da harkokin kasuwar lafiya za a kammala komai cikin Masara kamar yadda aka saba a kowa ce shekara.

“Gudanar da kasuwar duniya ba wani bakon al’amari ba ne mun saba aiwatar da shi a kowace shekara ayi cikin nasara da walwala kowa na jindadi da yi wa Allah godiya bukata ta biya nufi, tattalin arzikin kowa ya karu, Jihar Kaduna da Najeriya a matsayin kasa ta karbi bakuncin jama’a da kamfanonin da suka samu halartar cin kasuwar sun cimma bukatunsu na alkairi don haka a wannan shekarar ma an kara inganta tsarin da zai taimaki jama’a yan kasa da baki”, inji Fatima.

Don haka a madadin kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna, muna yin kira da fadakarwa ga kowa da suka hadar da Kamfanoni, Bankuna, cibiyoyin kasuwanci,yan kasuwa, ma’aikatu da bangarorin Gwamnati da masu bukatar zuwa kasuwar duniya da azo a gudanar da duk harkoki da kulla hudda ta saye da Sayarwa da kasuwanci cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin arziki ya ci gaba da inganta, kasancewar an yi tanajin dukkan abin da ya dace a samu na ci gaba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban kwamitin tsaro na kasuwar Kanar Jibril Hassan mai ritaya, cewa ya yi a matsayinsa na shugaban kwamitin tsaro sun je wurin dukkan hukumomin tsaron da ke Jihar Kaduna kuma sun nemi taimakonsu sun kuma ba su tabbacin aiwatar da aikinsu kamar yadda ya dace don haka nema za a ga jami’an tsaro masu yunufan da farin kaya na boye duk a ciki da wajen kasuwar.

Saboda haka “muna ba dukkan mahalarta wannan kasuwa tabbacin samun ingantaccen tsaro don haka kada kowa ya samu wata fargaba komai zai ta fi cikin nasara tun daga farko zuwa karshen gudanar da kasuwar cikin ikon Allah ba matsala”.

Da wakilin mu ya zagaya kasuwar ya ganewa idanunsa irin yadda kamfanoni, Bankuna, ma’aikatu da hukumomin Gwamnati gami da yan kasuwa daga wurare daban daban suke Tururuwa suna sauke kayansu da suka halarci kasuwar tare da dukiyar ta su, wanda hakan ke bayar da tabbaci lallai komai lafiya an fara kalau za kuma a kammala cikin nasara.

Wakilin namu ya kuma kira wadansu bangarorin Gwamnatin tarayya duk sun bayar da tabbacin halartar kasuwar domin kuwa sun ce suna nan a kan hanya, wasu kuma sun shaida mana cewa tuni jami’ansu na cikin kasuwar ta duniya.

Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kasuwanci

Farashin kayan abinci daga kasuwar Anchau ta jihar Kaduna

Published

on

Daga Idris Umar, Zariya

Farashin kayan abinci a jiya 23th April 2024

Masara
Me aure dubu 47 – 45 – 44
Marar aure dubu 42 – 41- 40

Farin wake
Dubu 90k 85k 80k

Waken suya
Dub 50k

Dawa
Dubu 43k 40k

Barkwano
Dubu 60k 57k

Tattasai
Busasshe dubu 70

Tumatir busasshe dubu
Dubu 70k

Tarugu
Dubu 45k 43k

KU KUMA KARANTA: Farashin kayan abinci a wasu kasuwanni a wannan makon

Shambo
Dubu 28k 27

Shinkafa me bawo
Dubu 40k 38k

Kwalin sugar mazarkwaila
Dubu 27k 26k
Karami dubu 17k 16k

Taki urea dubu 31k 30k
Indorama npk dubu 40k

Npk magic dubu 38k

Cement
Dubu 7100

Dauro
Dubu 55k 53k

Buhun fulawa
Dubu 53k

Buhun sugar
Dubu 77k

Kwalin taliya
Dubu 12,500

Indomie
Chaerie dubu 10,800
Supreme dubu 10,700

Macaroni dubu 12,500

Buhun dabino
Dubu 177k – 160k

Goriba
Dubu 13k – 12k

Kwanon rufi
Dubu 65 – 63

Abincin dabbobi

Dusa na inji menauyin 75kg Dubu 23 – 22k

Dusa tankaɗaɗɗiya menauyin 50kg dubu 14,000k

Garin Ɗorawa menauyin 65kg dubu 13k 14,500k

Kowa menauyin 35kg dubu 8k – 9k

Bincike da ƙwaƙƙwafi
Sarkin kasuwar Anchau

Continue Reading

Kasuwanci

Farashin kayan abinci a wasu kasuwanni a wannan makon

Published

on

Daga Idris Umar, Zariya

A kasuwar Bokkos da ke Jos, ranar Alhamis an sai da jar masara buhu ɗaya 50,000
Fara 48,000

Acca kwano ɗaya 3,200
Manya fara 3,100.

A kasuwar Mangu masara an sai da buhu ɗaya 51,000.

Haka aka sayar a kasuwar Barikin Ladi.

Kasuwar Azare jiya Lahadi.
An sayar da Dawa ja 56,000
Fara 54,000

Gero 56,000

Wake 95,000 zuwa
100,000.

Rogo busashshe 30,000 buhu ɗaya.

An sayar da buhun tsamiya 12,500.

An sayar da gyaɗa mai kwanso 30,000 buhu ɗaya.
Haka farashin ya kasance jiya a kasuwar Jama’are da kasuwar Sakuwa.
Shinkafa kuwa kwano ɗaya ‘yar ƙasa daga 3,000 ne zuwa 3,400.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya na fatan bunƙasa kasuwanci da Saudiyya zuwa dala biliyan 30

Da muka leƙa kasuwar dabbobi kuwa an yi jugum-jugum tsakanin mai saya da mai sayarwa kowa yana kukan tsadar rayuwa.

Da ya ke jajiberan sallace kasuwar ta cika maƙil da mutane.

A kasuwar kaji kuwa hada-hada kawai ake yi tsakanin masu kawo kaji daga karkara zuwa masu saya su kai birane.

Ƙaramar kaza ita ce naira 1000
(ɗan tsako kenan) amma manyan kaji sun kai 7,000 zuwa 8,000 har zuwa 10,000.

Allah ya kawo mana sauƙi.

Amma kamar wasu kayan abincin suna ɗan rage kuɗi.

Tsaraba daga abokin aikina Idris Ibrahim Azare

Continue Reading

Kasuwanci

Matatar mai ta Ɗangote ta soma sayar da fetur a Najeriya

Published

on

Matatar mai ta Ɗangote da ke Najeriya ta fara sayar da fetur a ƙasar a ranar Talata, in ji ƙungiyar tallatawa da sayar da mai ta kamfanin.

Wannan babban matakin tsayawa da ƙafafu ga Najeriya wajen biyan buƙatar makamashi da take da ita.

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka Aliko Ɗangote ne ya gina matatar man, mafi girma a nahiyar a gaɓar tekun Legas kan dala biliyan 20, kuma an kammala aikin bayan tsaiko na shekaru da dama da aka samu.

Matatar na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 kowace rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

Daraktan rukunan kamfanonin Dangote Devakumar Edwin ya tabbatar da cewa sun fara sayar da man dizel da man jiragen sama a ƙasar.

Edwin ya shaida wa Reuters cewa “Muna da isasshen mai. Ana jigilar man ta ruwa da ƙasa. Jiragen ruwa na bin layi ɗaya bayan ɗaya don ɗiban dizel da man jiragen sama.”

“Jiragen ruwa na ɗaukar lita miliyan 26, amma muna ƙoƙarin ganin an kawo jiragen da ke ɗaukar lita miliyan 37 don sauƙaƙa ayyukan.”

Ƙungiyar masu sayar da man ta amince kan sayar da kowacce litar dizel naira 1,225 bayan ƙulla yarjejeniya kan tsayar da farashi, in ji Abubakar Maigandi, Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur Mai Zaman Kanta a Nijeriya.

Mambobin ƙungiyar na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin Najeriya, in ji Maigandi.

Matatar mai ta Dangote na so ta kawo ƙarshen dogaro ga man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje da Najeriya ke yi.

Najeriya ce ƙasar da ta kowace yawan jama’a a Afirka, kuma tana kan gaba a tsakanin ƙasashen da ke fitar da albarkatun mai, amma tana sayo mai daga waje saboda ba ta da matatu.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like