Adam Muhammad Namadi Zai Fafata Da Duk Wani Dan Takara – Umar

0
282

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana dan takarar neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya karkashin PDP daga mazabar Kaduna ta tsakiya a Jihar Kaduna Adam Muhammad Namadi Sambo da cewa mutum ne da yake a shirye domin fafatawa da kowa ne dan takara.

Malam Umar da ya wakilci dan takarar wajen karbar takardar satifiket na shaidar cewa an tantance shi a matsayin dan takarar karkashin jam’iyyar PDP daga mazabar Kaduna ta tsakiya, ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan gabatar da wakilcin karbar takardar satifiket din bayan tantance Adam Muhammad Namadi a matsayin dan takara wanda kwamitin da uwar jam’iyya ta kasa ta aiko Kaduna domin aiwatar da aikin.

“Ai tun da dai an ba matasa damar yin takara hakika dan takara Umar Muhammad Namadi a shirye yake domin fafatawa da kowa a wannan tsarin”. Inji Umar.

Jam’iyyar PDP ta kasa ce ta aiko da wani kakkarfan kwamiti da suka zo Kaduna domin tantance yan takarar neman kujerar majalisar wakilai ta kasa da majalisar Dattawa daga Jihar Kaduna karkashin PDP.

Leave a Reply