Mun Janye Dakatarwar Da Muka Yiwa Shugaban Karamar Hukumar Bichi – Inji Kansiloli

0
350

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN majalisar dokokin Karamar hukumar Bichi Malam Mohammed Rabo Tinki ya bada sanarwar dage dakatar wa da aka yiwa shugaban Karamar hukumar watau Dokta Yusuf Mohammed Sabo na tsawon watanni 3 saboda daidaito da aka samu tsakanin Shugaban da kansilolin.

A cikin wani jawabi da ya yi a karshen zaman sulhun da aka gudanar, Malam Rabo Tinki ya ce ” Saboda samun fahimtar juna da muka yi tsakanin mu da Shugaban Karamar hukumar Bichi Dokta Yusuf Mohammed Sabo, mun janye dakatarwa da muka yi masa ba tare da tsaiko ba, Kuma muna jaddada cewa za muci gaba da tafiya tare bisa jagorancin sa domin samun ci gaban wannan yanki namu” inji shi.

Haka Kuma kansilolin sun bayyana cewa Dokta Sabo shi ne shugaban Karamar hukumar Bichi Kuma babu sauran wata matsala tsakanin su da bangaren zartaswa musamman ganin cewa, yanzu an fahimci juna kuma za a ci gaba da tafiya cikin nasara da mutun ta juna.

A nasa tsokacin, daraktan mulki na Karamar hukumar Wanda Kuma shi ne akawun majalisar dokokin karamar hukumar Alhaji Lawal Abdullahi Dala ya sanar da cewa ” sakamakon sasantawa da samun maslaha tsakanin majalisar dokokin karamar hukumar Bichi da zababben shugaban karamar hukumar, an janye dakatarwar da aka yi masa kuma komai ya koma daidai babu wata matsala”.

Darakta Lawal Dala ya Kara da cewa bisa samun wannan daidaito, Dokta Yusuf Mohammed Sabo da majalisar dokokin karamar hukumar Bichi tuni suka ci gaba da aiyukan su na alheri ga al’ummar karamar hukumar tare da jaddada cewa ba sauran wata matsala tsakanin bangarorin biyu.

Wakilin mu wanda ya sami magana da shugaba Dokta Yusuf Mohammed Sabo, ya ruwaito cewa shugaban Karamar hukumar ta Bichi ya jaddada cewa zai ci gaba da yin aiki da majalisar dokokin karamar hukumar kamar yadda aka saba domin samarda ci gaba mai albarka a fadin yankin.

Leave a Reply