Shigar Dokta Wailare PDP Ta Kara Wa Jam’iyyar Karfi Da Magoya Bay – Inji Al’ummar Yankin

0
493

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AL’UMMAR kananan hukumomin Dambatta da Mokoda sun bayyana cewa Jam’iyyar PDP tana kara karfi da samun magoya baya tun lokacin da Dokta Saleh Musa Wailare ya koma cikin ta kamar yadda kowa yake gani a yau.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Dokta Saleh Musa Wailare ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP inda kuma komawar tasa ta haifar wa jam’iyyar ta PDP alheri duba da yadda matashin dan siyasar ya bunkasa wannan jam’iyya ta PDP a kananan hukumomin Dambatta da Makoda.

Haka kuma sun sanar da cewa Dokta Saleh Wailare dan siyasa ne mai matukar kaunar ci gaban al’umma, sannan yana gudanar da harkokin sa na siyasa ne bisa sanin ya kamata wanda hakan ta sanya mutane suke biye da shi saboda kyawawan manufofin sa.

Mafiya yawan mutanen da suka zanta da wakilin mu, sun bayyana cewa siyasa irin ta Dokta Saleh Musa Wailare irin ta ake bukata domin idan aka zabe shi zuwa majalisar wakilai ta kasa ko shakka babu za’a sami dukkanin wata ribar dimokuradiyya da ake bukata a 2023.

Kididdiga ta nuna cewa yanzu jam’iyyar PDP ta sami karuwar magoya baya da kashi 45 daga cikin dari, sannan a kowace rana ana samun wadanda suke shigarta daga sauran jam’iyyu musamman mata da matasa masu jefa kuri’a, kana mafiya yawan wadanda suke komawa jam’iyyar ta PDP sun bayyana cewa saboda Dokta Saleh Musa Wailare suke shigarta domin shine yake da kishin al’uma a tsarin dimokuradiyya.

Leave a Reply