‘Abubuwan da zan riƙa tunawa da su game da ‘yata Hanifa da aka kashe’

0
466

Hanifa

An sace Hanifa ne a kan hanyarta ta zuwa makaranta

Daga Rabo Haladu

Dangi da ƴan uwan yarinyar nan Hanifa da ake zargin malaminta ya sace tare da kashe ta, kana ya binne gawarta a gidansa a jihar Kano na ci gaba da alhinin rasuwarta.

Ranar Alhamis rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da gano gawar Hanifa Abubakar a wani kabari da aka binne ta bayan an kashe ta.

Cikin kuka da hawaye, mahaifin Hanifa, Malam Abubakar Abdussalam, ya shaida cewa sun shiga cikin mummunan tashin hankali sakamakon lamarin da ya faru, har ta kai ga an kwantar da mahaifiyar marigayiyar a asibiti.

“Lokacin da mahaifiyar ta samu labari ta kaɗu, mun kai ta asibiti yanzu haka an sa mata ruwa an ba ta magunguna, ba ta iya ko cin abinci kullum sai kuka, ni kaina bana iya cin abinci ba na iya barci,” in ji shi.Ya ƙara da cewa “Ina ofishin Hukumar DSS aka kirawo ni aka sanar da ni cewa ga shi an gano gawarta, don haka suka ba ni haƙuri suka ce ƙaddara ce daga Ubangiji inyi haƙuri.”  ‘zan riƙa tuna Hanifada su’boda Malam Abubakar ya shaida  cewa ƴarsa Hanifa yarinya ce mai haba-haba, kullum fuskarta cikin annuri ba ta da wata matsala kuma mutane da dama da suka san ta za su shaida hakan.

“Hanifa yarinya ce da duk wanda ya san ta a unguwa makwabta da dangi ya san cewa tana da basira da hazaƙa, ba wanda take so kamar babanta, kuma yanzu ga halin da ta rasu a ciki,” a cwewarsa.

Sai dai ya ce ya yi imanin cewa abun da ya faru jarraba ce daga ubangiji. ”Shi dama ubangiji yana da hanyoyin jarrabarsa da abubuwa da yawa, don haka wannan line jarabawa ce” in ji shi.

‘Maganata ta ƙarshe da Hanifa’

”Magana ta ƙarshe da na yi da ita ce wadda na yi da ita ranar da za a sace ta, ta zo za ta tafi makaranta mahaifiyarta ta ce Hanifa ba ki yi addu’a ba, ta ce na yi, ta sake yi tana cewa ‘Bismillahi Tawakkalt Alallah’, tana yi da ƙarfi don ta ji cewa ta yi ɗin, ina ce mata to Hanifa kin yi, na yadda kin yi yanzu, ta tafi ta je tana sallama da mahaifiyarta, tana ce mata tun da za ki tafi kasuwa idan kin je ki taho min da alewar madara ina son zan yi sadaka da hannuna,” a cewar Malam Abubakar.

Ya ce lokacin da ya samu labarin an kama mutumin da ya sace ta ɗin ya ji daɗi, bisa tsammanin cewa zai nuna wurin da ya ɓoye ƴarsa, amma daga baya sai ya ji abun da ya saɓa da hakan.

Ya kuma shawarci iyaye su ƙara zage dantse wajen kula da ƴaƴansu, sannan a ci gaba da addu’ar Allah ya ba da zaman lafiya mai ɗorewa.

Leave a Reply