Ayyukan Gwamna El-Rufa’i Sun Sanya Na Kasa Gane Hanyar Gidana A Kaduna – Buhari

0
304

Daga Wakilinmu

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan ci gaban da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i ya yi sun sa ya kasa kai kanshi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya kaddamar da ayyukan hanyoyi da gadoji da sauran ayyukan more rayuwa a yankin Kafanchan dake kudancin Kaduna da kuma wasu ayyukan a kwaryar garin Kaduna, ya ce Kaduna ta canza fasali karkashin Gwamna Nasiru Ahmed El-rufa’i.

Da yake jawabin a wajen kaddamar da hanyoyin da gwamna El-Rufa’i ya gyara, Shugaba Buhari ya ce Kaduna gida ce a gurin shi amma yanzu da kyar ne ya gane gidan shi sabili da yadda hanyoyin suka sauya fasalin birnin Kaduna.

Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna
Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna

Tuni dai Jam’iyyar PDP mai adawa a jahar Kaduna ta yi marhaban da zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kaduna, amma ta ce ziyarar siyasa ce tsantsa kuma ta kalubalanci gwamna El-rufa’i ya wuce yankin Birnin Gwari da Giwa don jajantawa mutanen da ke fama da hare-haren ‘yan-bindiga a yankin.

A hirarshi da Muryar Amurka, Alh. Ibrahim Aliyu Wusono, sakataren Jam’iyyar ta PDP a jahar Kaduna ya ce a da shugaba Buhari ya ce baya yawon kaddamar da ayyukan da gwamnoni ke yi domin abinda aka zabe su su yi ke nan. Ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya je ya ziyarci wadanda suka yi fama da tashin hankalin da ake fuskanta a kasa baki daya ta matsalar tsaro amma ba ya buge a kaddamar da hanyoyi ba.

Sai dai kuma Jam’iyyar APC mai mulki ta ce gajiyawa ce ta sa Jam’iyyar PDP ke korafi game da ayyukan da gwamnatin APC ta yi duk da cewa koya yana yaba yadda babban birnin jihar ya sake.

Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna
Shugaba Buhari yana kaddamar da aikin hanyoyi a Kaduna

A hirarshi da Muryar Amurka, sakataren yada labaru na Jam’iyyar, Alh. Salisu Tanko Wusono ya ce, bai kamata a rufe ido a ganin ci gaban da aka samu ba, a rika neman bincika kudin da aka kashe kan aikin da kowa yana iya gani a kasa a zahirance duk da cewa akwai wadansu ayyukan da ba a kammala ba.

Ziyarar aiki ta shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jahar Kaduna dai ta kwanaki biyu ce, inda a daren nan zai halarci taron cin abuncin dare sannan gobe Juma’a kuma ya wuce Zariya don karkare kaddamar da ayyukan da gwamnatin Kaduna ta yi cikin shekaru shida da wasu watanni.

Aikin hanyoyin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Kaduna
Aikin hanyoyin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Kaduna

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here