Abubakar Ibrahim Abdullahi Ne Gwarzon Musabakar Jihar Kaduna

0
477

Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna

BAYAN gudanar da gasar musabakar karatun Alkur’ani ta bana shekarar 2022 da aka yi a babban dakin taro na Alhaji Ahmadu Chanchangi a unguwar Kinkinau cikin garin Kaduna da Alkalai tare da wasu makaranta Kur’ani da suka fafata an dai sanar da Abubakar Ibrahim Abdullahi a matsayin Gwarzon musabakar na wannan shekara.

Abubakar Ibrahim Abdullahi ya samu nasara ne bayan fafatawa a jerin daliban da suka samu shiga gasar a izifi Sittin (60).

Kamar yadda wakilinmu ya tattauna da Gwarzo Abubakar Ibrahim Abdullahi, ya shaida mana cewa an haife shi ne a shekarar 2001 Kuma ya zo ne daga Gundumar Rigasa a karamar hukumar Igabi dake cikin Jihar Kaduna.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da Sanya shi a cikin addu’a kasancewar sa wanda zai wakilci Jihar Kaduna a gasar ta kasa da za a yi nan gaba.

Ya kuma bayyana cewa hakika karatu da haddar Kur’ani ba karamin al’amari ba ne domin kuwa sai mutum ya dage sossi.

Abubakar ya ce ya yi matukar farin ciki kwarai da wannan nasarar da Allah ya bashi.

Sai kuma Zainab Tanimu Zailani da ta samu nasarar kasancewa ta biyu a jerin wadanda suka fafata a Izifi biyu.

Da ta yi kira ga yan uwanta mata da su ci gaba da dagewa wajen kokarin yin haddar alkur’ani mai girma ta yadda za a dace da babban rabo duniya da lahira.

An dai samu wadansu bayin Allah da suka bayar da kyautar kudi naira miliyan biyar da wadanda suka zo na daya a bangaren Maza da Mata, Alkalai da kuma yan kwamitin musabakar.

Sai kuma gudunmawar kudi naira miliyan uku da aka ce kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na Jihar Kaduna ne ya bayar da miliyan uku.

An kuma yi wa’azi da fadakarwa daga malamai da sauran shugabannin al’umma, har aka bayyana cewa an samu nasarar da ba a taba samu ba a gasar musabakar.

An kuma samu gagarumin hadin kai tsakanin kungiyar Izala da Fityanul Islam, wanda Samuwar hakan ba karamar nasara ba ce.

Leave a Reply