A Rika Yin Gwajin Ciwon Sanyi, Kafin Ayi Daurin Aure- Dokta Wase

0
349

Daga; Isah Ahmed, Jos.

DOKTA Abdullahi Abdullahi Wase, Wani fitatcen mai maganin gargajiya ne, da ke zaune a garin Sabon garin Narabi da ke Karamar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi. 

A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana mahimmancin maganin gargajiya. Haka kuma ya kawo shawarar a rika yin gwajin ciwon sanyi, kafin a daura aure, kamar yadda ake yin na wasu cututtuka.

Ga yadda tattaunawar ta kasance

GTK: A wanne lokaci ne ka fara wannan sana’a ta maganin gargajiya?

Dokta Wase: A kalla na kai kamar shekara 20, ina yin wannan sana’a ta maganin gargajiya. Kuma na fara wannan Sana’a ne tun daga mahaifata ta garin Wase. 

GTK: A wanne bangaren jinya ne, kafi mayar da hankali?

Dokta Wase: Gaskiya saboda yanzu duniya tana fama da larurar sanyi wanda yanzu wannan larura ta zama ruwan dare a cikin al’umma maza da mata, manya da kananan yara, har da jira jirai, suna fama da wannan larura.  Don haka nafi mayar da hankali, wajen bayar da maganin wannan larura, kuma muna jinyar rashin haihuwa da abin da ya shafi matsalar gaban namiji dai sauransu.

GTK: A ina ne kuke zaune?

Dokta Wase: Ada hekwatarmu tana cikin garin Jos ne, amma saboda matsalolin rikice rikice da aka yi fama da su  a wannan gari, ya sanya muka koma Sabon garin Narabi, dake Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

GTK: Daga lokacin da ka fara wannan sana’a, zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne ka samu?

Dokta Wase: Gaskiya mun sami nasarori da dama a wannan sana’a. Domin ta dalilin wannan sana’a nayi aure na gina gida nayi aikin Hajji na mallaki kadarori masu tarin yawa. 

Kuma a kalla yanzu ina da ma’aikata sama da mutum 20, da suke taimaka mani, wajen gudanar da wannan sana’a.

Haka kuma akwai mutane da dama da suka yi shekara da shekaru, basu sami haihuwa ba, amma cikin ikon Allah sun sami haihuwa, sakamakon maganin da muka basu.

GTK: Kamar daga wadanne wurare ne kake samun masu jinya?

Dokta Wase: Muna samun masu jinya daga wurare daban daban, har daga kasashen waje. Misali a nan Najeriya muna samun masu jinya kamar daga jihohin Barno da Adamawa da Taraba da Filato da Bauchi da Kaduna da Kano da Jigawa da Legas da Oyo da Cross Rivers. Kuma  kamar daga kasashen waje, muna samun masu jinya kamar daga Kamaru da Chadi da Gabon da dai sauransu.

GTK: Wace shawara ce zaka baiwa al’umma, kan larurar ciwon sanyi?

Dokta Wase: Babbar shawarar da muke bayarwa ita ce, ya kamata yanzu idan za a yi aure, mace ko namiji a rika gwajin ciwon sanyi, kamar yadda ake yin na sauran cututtuka. Domin idan akwai larurar ciwon sanyi, a jikin namiji ko mace, idan aka sadu za a iya yadawa juna. 

GTK: Wanne irin mahimmanci ne, maganin gargajiya yake da shi?

Dokta Wase: A duniya baki daya zamu iya cewa maganin gargajiya yafi maganin zamani mahimmanci. Sai dai matsalar wasu masu maganin gargajiya ne, basu dauki abin da mahimmanci ba. 

Amma mahimmancin da maganin gargajiya yake da shi, ba za a kwatanta shi da maganin zamani ba domin kasashen da suka cigaba, kamar China da Indiya suna amfani da maganin gargajiya fiye da maganin zamani. 

GTK: Wanne kira ne kake da shi, zuwa ga gwamnatin Najeriya, kan maganin gargajiya?

Dokta Wase:  Allah ya albarkaci Najeriya da itatuwa iri daban daban. Idan muka yi amfani da wadannan itatutuwa kamar yadda ya kamata, duniya zata amfana. Yanzu kamar China suna zuwa nan Najeriya suna dibar itatuwa kamar Maringa da tafasa da citta suna tafiya da su zuwa kasarsu, suna yin magani da su. 

Da a ce Najeriya ta san abin da take da shi kan maganin gargajiya, da ba zata tsaya tana dogara da man fetur ba musamman a Arewacin Najeriya, don haka ina kira ga gwamnatin Najeriya ta rungumi maganin gargajiya. 

Leave a Reply