EFCC a Legas ta kama ‘yan damfara 792

0
28
EFCC a Legas ta kama ‘yan damfara 792

EFCC a Legas ta kama ‘yan damfara 792

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta kama mutane 792 da ake zargi da damfara a Jihar Legas, ciki har da ‘yan ƙasashen Larabawa, China, da Philippines.

Wannan shi ne mafi girman kamen da hukumar ta yi a rana guda.

Daraktan Hulɗa da Jama’a na EFCC, Wilson Uwajaren ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Legas.

A cewarsa, wadannan ‘yan damfara suna amfani da yanar gizo don cutar mutane, musamman ta hanyar yin soyayya ta karya don samun kudi daga jama’a a sassan duniya.

An kama su ne a ranar 10 ga watan Disamba a wani katafaren gida mai hawa bakwai da ke Victoria Island, a Legas.

Uwajaren, ya ce hukumar ta shafe watanni tana tattara bayanai kafin kai samamen.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai:
‘Yan China 148, ‘Yan Philippines 40, ‘Yan Khazakhtan 2, Ɗan Pakistan 1, Ɗan Indonesia 1.

KU KUMA KARANTA: FBI ta Amurka, ta cafke wani ɗan Najeriya kan zargin damfarar dala miliyan 6 ta Intanet

Waɗannan ‘yan damfara sun ɗauki ‘yan Najeriya aiki tare da biyan su sama da Naira 200,000 a kowanne wata domin taya su gudanar da ayyukansu na damfara.

An gano manyan kwamfutoci da layukan waya sama da 500 a cikin ginin, inda aka fi samun kayan aiki a hawa na biyar.

Mutanen da suka fi fadawa tarkon waɗannan masu damfara sun haɗa da Amurkawa, ‘yan Canada, da ‘yan Mexico.

Haka nan, ‘yan damfarar suna amfani da layukan waya daga ƙasashen Turai kamar Jamus da Italiya don yin ayyukansu cikin sauƙi.

Leave a Reply