Gwamnatin Kano ta Sanya dokar Noma ta shekara Biyar ga duk Wanda aka kama da satar waya
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gwamnatin Kano tace Duk Wanda aka Samu Da Laifin Satar Waya Ko Harkar Fadan Daba Ta Wajabta Masa Yin Noma Na Shekaru Biyar Batare Da zabin tara ba.
Tunda Dai ana Zargin akwai Masu Daure Musu Gindi Suke Hallaka Wadanda Basu jiba ba Su Gani ba a Cikin Al’umma
Gwamnatin Sai Ta Samar da Cibiyoyi a wasu Yankunan Jihar Ta Kano Da Zasu Rika kula Da Wadannan Matasa da aka Kama Da Laifin Daba Da Kwacen Waya
KU KUMA KARANTA:Masu ƙwacen waya a Kano sun kashe ɗalibin Jami’ar Bayero
A cikin Shekaru biyar da Zasuyi Suna Noma za Kuma a rika Koya Musu Ilimin addini Da na Zamani Domin Dawo da Hankalinsu jikinsu
Bayan Sun kammala Shekaru Biyar Suna Noma Sai Gwamnatin Ta basu Wasu Daga Cikin Kudin da aka Sayar Da Kayan Amfanin Nomansu kuma ayi Musu auren Gata
Idan Har Gwamnatin Tayi Amfani Da Wannan Tsari Insha allahu Sai ka nemi Dan Daba Ko Mai Ƙwacen Waya a kano Ka rasa Domin Yana Can Yana Noman Dole Da Kuma Samun Tarbiya.