An kama mutane 5 da ake zargi da kisan ‘yan Kano 2 a Benuwe

0
27
An kama mutane 5 da ake zargi da kisan 'yan Kano 2 a Benuwe

An kama mutane 5 da ake zargi da kisan ‘yan Kano 2 a Benuwe

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jami’an ’yan sanda a jihar Benue sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin jihar Kano a garin Agan da ke kusa da Makurdi.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Benue, Sir Tersoo Kula, ya fitar ranar Talata, 24 ga Yuni, 2025.

KU KUMA KARANTA: Jagororin muslumi a Benuwe sun yi taron gaggawa kan kisan gillar musulmi a jihar

Sanarwar ta bayyana cewa kama wadannan da ake zargi ya biyo bayan umarnin da gwamna Rev. Fr. Hyacinth Alia ya bai wa kwamishinan ’yan sanda da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da an kamo masu hannu a cikin lamarin.

Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin abin ƙyama da rashin imani, yana mai jaddada cewa sai an hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ya kuma miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, da iyalan marigayan.

Leave a Reply