Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Yobe, Hajiya Fatima Mairiga ta rasu
Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Hajiya Fatima Umar Mairiga, ta rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
Hajiya Mairiga ta rasu ranar Asabar a Kano, inda ta je Asibiti domin a duba lafiyar ta.

An sanar da rasuwarta ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hussaini Suleh, ya fitar, wanda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga iyalan jam’iyyar APC a jihar.
A cewar sanarwar, jigo a APC ta rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
Ku kuma karanta: A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa
“Hajiya Fatima Mairiga, Mataimakiyar Shugabar Mata ta na jam’iyyar APC a Jihar Yobe, ta rasu ranar Asabar a Kano bayan wata gajeriyar rashin lafiya,” in ji sanarwar.
Ko da yake ba a bayyana yanayin rashin lafiyarta ba, mutuwarta ta jefa ‘yan’uwa, abokan siyasa da magoya baya cikin makoki.
Sanarwar ta kuma sanar da cewa za a yi jana’izar marigayiyar a babban Masallacin Damaturu (Yobe Mosque and Islamic Center), babban birnin Jihar Yobe, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, bisa ga bisa koyarwar addinin Musulunci.


