‘Yan bindiga sun sace alƙalin babbar kotun jihar Kebbi
Rahotanni daga jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, ‘yan bindiga sun sun yi garkuwa alƙalin babbar kotun jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruƙu Hassan Bunza.
Wani mazaunin jihar Kebbi, ya bayyana ra’ayinsa da cewa “babu wani abin damuwa a ciki tun da shi mai girma Gwamna duk hanyoyin da ake bi a karɓo mutane a hannun ‘yan bindiga ya sani, ko yanzu hanyar da aka bi aka karɓo ‘Deputy Speaker’ da hanyar da aka bi aka karɓo ɗaliban makarantar Maga har wa yau au ita zai bi ya karɓo wannan Alƙalin”.
Ku kuma karanta: Farfesa Mansur Yelwa ya sauka daga limancin masallacin jami’ar ATBU
Ya zuwa yanzu dai ana ta zaman zullumi a jihar, don jin meye zai biyo bayan sace alƙalin alƙalan.


