Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeLabariMataimakiyar Shugabar Mata...

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Yobe, Hajiya Fatima Mairiga ta rasu

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Yobe, Hajiya Fatima Mairiga ta rasu

Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Hajiya Fatima Umar Mairiga, ta rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Hajiya Mairiga ta rasu ranar Asabar a Kano, inda ta je Asibiti domin a duba lafiyar ta.

An sanar da rasuwarta ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hussaini Suleh, ya fitar, wanda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga iyalan jam’iyyar APC a jihar.

A cewar sanarwar, jigo a APC ta rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Ku kuma karanta: A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa

“Hajiya Fatima Mairiga, Mataimakiyar Shugabar Mata ta na jam’iyyar APC a Jihar Yobe, ta rasu ranar Asabar a Kano bayan wata gajeriyar rashin lafiya,” in ji sanarwar.

Ko da yake ba a bayyana yanayin rashin lafiyarta ba, mutuwarta ta jefa ‘yan’uwa, abokan siyasa da magoya baya cikin makoki.

Sanarwar ta kuma sanar da cewa za a yi jana’izar marigayiyar a babban Masallacin Damaturu (Yobe Mosque and Islamic Center), babban birnin Jihar Yobe, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, bisa ga bisa koyarwar addinin Musulunci.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

An yi jana'izar 'yan Shi'a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba'een a Abuja 'Yan'uwa Musulmi, Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da jana'izar 'yan'uwa biyar a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ranar Laraba,...

Miliyoyin ‘Yan’uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba’een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS)

Miliyoyin 'Yan'uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba'een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS) Miliyoyin 'yan'uwa Musulmi na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun fara tattakin Yaumul Arba'een na na Imam Husaini (AS) wanda suka saba...

‘Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe ‘yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata

'Yansanda a Katsina sun kama magidancin da ya kashe 'yarsa, don ta ƙi amincewa da mijin da ya zaɓa mata Rundunar 'yan sandan ta bayyana mutumin a matsayin Kabir Sani mazaunin unguwar rukunin gidajen 'Shagari Low-Cost'. 'Yansandan sun ce maƙwabtan Kabir...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.