Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeLabariAn yi jana'izar...

An yi jana’izar mataimakiyar shugabar Mata ta Jam’iyyar APC, Hajiya Mairiga

An yi jana’izar mataimakiyar shugabar Mata ta Jam’iyyar APC, Hajiya Mairiga

Jihar Yobe ta shiga cikin makoki bayan rasuwar Hajiya Fatima Mairiga, fitacciyar mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC kuma ‘yar siyasa mai daraja da kima, wacce ta rasu a Kano.

A cikin sanarwar manema labarai da Hussaini Mai Sule, Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Yobe ya fitar, ya ce, an binne mamaciyar a Damaturu ranar Lahadi bayan an yi mata sallar jana’iza a Masallacin Yobe Mosque and Islamic Center, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.

Jana’izar ta samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, ‘yan’uwa, da abokai.

Ku kuma karanta: Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Yobe, Hajiya Fatima Mairiga ta rasu

Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Idi Barde Gubana, wanda ya jagoranci manyan mutane a jana’izar, tare da rakiyar tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Sanata Ibrahim Gaidam, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Hon. Chiroma Buba Mashio.

Sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da kwamishinoni, ‘yan majalisa, masu ba da shawara na musamman da masu ruwa da tsaki na APC, suma sun halarci jana’izar.

Mataimakin Babban Limamin jihar Yobe, Sheikh Mohammed Ali Goni Kamsulum ne ya jagoranci sallar jana’izar.

Da yake magana kan rasuwar Hajiya Mairiga, Mataimakin Gwamnan ya bayyana ta a matsayin ‘yar siyasa mai himma, mai taimakon jama’a kuma shugaba mai hazaƙa wadda ta yi tasiri sosai ga rayuwar mutane da yawa.

Ya ce marigayiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta ƙarfafa mata gwiwa da kuma ƙarfafa shigar mata cikin harkokin siyasa.

Hon. Gubana ya ce ba za a manta da gudunmawar da Hajiya Mairiga ta bayar ga ci gaban jihar da kuma mutanen da ta tallafa musu a lokacin rayuwarta ba.

Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta mata kurakuranta, ya karɓi kyawawan ayyukanta ya kuma sa Jannatul Firdaus ce makomar ta.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar, ciki har da dangi, abokan ta na siyasa da kuma dimbin jama’a, wadanda suka taru don yi wa marigayiyar addu’a.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a da sakamako mafi daraja

'Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari'a da sakamako mafi daraja Wata matashiya mai shekaru 24, Aisha Widad Yahaya, wadda ita ce uwa ga yaro ɗaya kuma matar aure, ta kafa...

An yi jana’izar ‘yan Shi’a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba’een a Abuja

An yi jana'izar 'yan Shi'a 5 da suka rasu a hatsarin mota a hanyar Tattakin Arba'een a Abuja 'Yan'uwa Musulmi, Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun gudanar da jana'izar 'yan'uwa biyar a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya ranar Laraba,...

Miliyoyin ‘Yan’uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba’een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS)

Miliyoyin 'Yan'uwa Musulmi A Nijeriya Sun Fara Tattakin Arba'een Domin Tunawa da Imam Husaini (AS) Miliyoyin 'yan'uwa Musulmi na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), sun fara tattakin Yaumul Arba'een na na Imam Husaini (AS) wanda suka saba...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.