Connect with us

Nishadi

Cece kuce akan yawan taliyar leda

Published

on

Rahotanni daga majiya me qarfi sun zo mana cewa an rage yawan taliyar Leda.

Wani matsahi ya gaya ma wakilan mu cewa, an zare guda hudu a ciki, sannan an rage mata kauri, kana an ƙarawa ledar iska??..Ba a tsaya anan ba, seda aka ƙara mata handaret naira?.

Mun sami labari cewa an zare tsinke 34 na taliyar leda, a gaskiya ba haka ba ne, domin bincken ya tabbatar mana da cewa tsinke sha takwas ake zarewa daga kamfani, inda masu shaguna kan zari tsinke hudu, jimillar abinda aka zare ya zama tsinke 24 kenan.

Domin kawo qarshen wannan cece kuce, muna bawa me karatu shawara ya siyo taliyar leda ya ƙirga da kansa, domin sanin taƙamaimai guda nawa ne a ciki?. Masu iya magana kance, ‘yi da kai, yafi saqo’.

Mudai daga Neptune, fatanmu, Allah Ya Kawo mana sauqin tsadar kayan abinci. Amin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Nishadi

Sadiya Haruna ta sake aure karo na 10

Published

on

Sadiya Haruna ta sake aure karo na 10

Sadiya Haruna ta sake aure karo na 10

Jarumar TikTok, Sayyada Sadiya Haruna ta sake amarcewa a ranar Juma’a watanni kaɗan da mutuwar aurenta da jarumin TikTok Al Ameen G-Fresh.

A wani kati da ta wallafa a shafinta na Instagram, Sadiya ta bayyana sunan angon nata a matsayin Hon. Babagana Audu Grema.

An daura auren ne da misalin ƙarfe ɗaya bayan sallar Juma’a kamar yadda katin ya nuna a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin tarayya ta bai wa Rahama Sadau muƙami

Auren na zuwa mako guda bayan da jarumar ta TikTok ta bayyana a shirin tattaunawa na jarumar Kannywood Hadiza Gabon “Gabon Talk Show” inda Sadiya ta caccaki G-Fresh tare da bayyana matsalolin da suka kai ga mutuwar aurenta da shi.

Auren har ila yau na zuwa ne kwana guda bayan da shirin na Gabon ya watsa tattaunawar mayar da martani da G-Fresh inda shi ma ya yi ta sukar tsohuwar matar tasa – mafi aksarin lokuta a kaikaice.

Continue Reading

Labarai

An haramta shirya fina-finan da ke nuna ƴan daudu da ƴan daba a Kano

Published

on

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta shirya fina-finai da ke nuna faɗan daba da harkar Daudu a Kano.

Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da hukumar ta tace fina-finan ta fitar a ranar Laraba.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan ta tattauna da ma’aikatan hukumar da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood waɗanda suka haɗa da ƙungiyoyin MOPPAN, Arewa Film Makers da daraktoci da kuma furodusoshi.

Abba ya ƙara da cewa doka ce ta bai wa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin ya ci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar da ke jihar.

KU KUMA KARANTA: Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

“Tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su ci gaba da yaɗuwa a cikin al’umma,” in ji shi.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta ɗauki matakin rufe gidajen gala a jihar inda ta ce har sai bayan azumin watan Ramadana.

Continue Reading

Nishadi

Ali Nuhu ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan kwaikwayo na Nollywood ‘Europe Golden Awards’

Published

on

Fitaccen jarumin nan na Najeriya Ali Nuhu wanda fitaccen jarumin fina-finan Kannywood ne, ya samu kyautar gwarzon ɗan wasa a ‘Nollywood Europe Golden Awards’.

Ali Nuhu na ɗaya daga cikin fitattun jaruman fina-finan Nollywood da na Kannywood wanda ya ɗauki hankulan mutane da dama a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Lambar Yabo

Ba wai mutanen Najeriya kawai ne suke son wasan kwaikwayonsa ba amma mutanen Turai da sauran ƙasashen waje.

Ali Nuhu yana da shekaru 49 ya samu nasarori da dama.

An san shi da tawali’u da himma a cikin aikinsa.

KU KUMA KARANTA: Rahama Sadau da Ali Nuhu sun jagoranci Fim ɗin Hausa na farko a Netflix don bunƙasa al’adun Arewa

Ya fito a fina-finai da dama da suka haɗa da garin Shanty da sauran fina-finai da dama waɗanda suka sa ya shahara sosai.

Mutane suna ƙaunarsa sosai kuma suna farin cikin ganin ya yi fice. Mutanen da suka ga rubutun nasa mintuna kaɗan da suka gabata suna taya murna saboda kasancewarsa gwarzon jarumin Nollywood a Turai Golden Awards a bana.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like