Ranar Yara: Zamu Ci Gaba Da Bunkasa Rayuwar Mata Da Yara Kanana – Inji Zainab Ali Musa

0
364

Daga; Jabiru Hassan.

JAMI’AR hulda da jama’a ta majalisar matan Nigeria  to kasa watau  “National Council For Women Societies” (NCWS), Hajiya Zainab Ali Musa ta bada shawara game Iyaye mata da su kara kokari wajen Kulawa da tarbiyyar yayan su ta yadda zasu ci gaba da kasancewa al’umma nagari.

Ta yi wannan tsokacin ne a ganawar su da wakilin mu dangane da zagayowar wannan rana ta yara wanda kuma majalisar dinkin duniya ta ware domin bukukuwa na musamman domin faranta zukatan yara a matsayin su na manyan wata rana.

Hajiya Zainab Ali Musa ta kara da cewa “akwai babban kalubale kan iyayen yara musamman ganin yadda zamani yake daukar sabon kalubale, wanda kuma wajibi ne Iyaye da masu rike da yara su rika sanin yanayin zamantakewar yaran su ko wadanda suke riko”. Inji ta.

Ta ce kungiyar su ta (NCWS) karkashin jagorancin Hajiya Lami Lau ta na kokari kwarai da gaske wajen kyautata rayuwar mata da yara kanana a kowane lungu da sako na kasarnan, sannan akwai bukatar ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu duk da irin kalubalen da duniya ta shiga wajen kyautata zamantakewa.

A karshe, Hajiya Zainab Ali Musa ta hori yara da su tsaya su nemi ilimi da dukkanin wasu hanyoyi na dogaro dakai musamman ganin yadda zamani yake canzawa ta kowane fanni.

Leave a Reply