Matsin Tattalin Arziki Ya Canza Najeriya – Sanata Walid Jibril

0
399

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.


SANATA Walid Jibril, Uban kungiyar  masu masaku a Najeriya na dindindin ya bayyana cewa sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fama da shi halin tattalin arzikin tarayyar Najeriya ya canza kwarai daga yadda aka san shi a can baya.

Sanata Walid Jibril ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar kasuwar duniya ta kasa da kasa da aka kammala kwanan nan a Kaduna.

Sanata Walid Jibril ya ce ai kamar yadda aka Sani ba sai an yi wani taliki ba irin yadda matsin tattalin arziki ya Sanya kasa da al’ummarta shiga cikin wani hali na daban da ba a saba da shi ba.

“Taimakon da ake samu daga Gwamnati ya yi dan sanyi a halin yanzu, musamman mu da muke da masaku a Najeriya baki, wanda ni ne uban wannan kungiyar masu masaku na dindin din a Najeriya baki daya don haka idan zamu ci gaba da yin lisaafin irin yadda lamarin ke kasancewa hakika sai mu dade mu na yi kuma abin ba zai yi kyau ba ko kadan”, inji Walid Jibril.

Danga ne da irin fannonin da yakamata a yi wa gyara kuwa sai Sanata Walid Jibril ya ce kamar yadda ya dace kamfanoni su yi ayyukansu, misali a yanzu ana maganar wutar lantarki da can baya ake yin amfani da ita cikin ruwan sanyi, amma a yanzu kuma sai dai ayi amfani da Janareton bayar da wuta ga tsadar man Gas ya yi yawa da sauran wadansu abubuwa duk babu su baki daya.

Sai kuma samun kayayyakin da za a yi aiki da su na kasar waje a Najeriya duk babu to yaya za a yi.

Walid Jibril, ya kuma yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta mayar da hankali sosai wajen magance abubuwan da suke damun kasar gwargwadon hali ta yadda jama’a za su samu natsuwa. 

Leave a Reply