Zaben 2023: ABG, Ya Fara Ziyarar Shugabannin PDP Na Unguwanni A Kaduna

0
534

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A YAYIN da Jam’iyyu ke shirin gudanar da zaben fidda gwani na zaben 2023, tsohon dan majalisar tarayya, Honarabul Shehu Bawa wanda aka fi sani da ABG ya fara ziyarar Mazabun unguwanni domin sanar da shuwagabannin Jam’iyyar PDP aniyar sa ta tsayawa takara a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa.

ABG ya fara ziyarar tuntubar ne domin sanar da Exco’s a hukumance a matakin kananan hukumomi da unguwanni tare wanda suka hada unguwar Liman, Mai Burji da Shaba, duk a Kaduna ta Arewa.

Yayin da yake ba da tabbaci ga shugabannin Jam’iyyar na kyakkyawan wakilci, ɗan siyasar ya bayyana tabbacin irin shirye-shiryen da yake da aniyar aiwatarwa ga dukkan masu ruwa da tsaki a muhimman shawarwarin majalisa idan aka zabe shi a 2023.

Ya kara cewa siyasa ta shafi yi wa jama’a hidima ne, tare da tabbatar da yakinsu, bukatu da jin dadinsu bisa kulawar da ake bukata.

Tsohon Dan Majalisar wakilai ya nemi goyon baya da kuri’un shugabannin wadanda za su zama wakilai a zaben fidda gwani, inda ya umurce su da su fifita sha’awar mazabu da jama’a fiye da amfanin kashin kai, yana mai cewa al’ummar yanzu da na gaba za su yi alfahari da kishin kasa da kishin ci gaban da suke da shi don ci gaban al’umma.

“Na zo nan ne domin in sanar da ku cewa na bayar da kaina a matsayin wakilin ku a majalisar wakilai a zaben fidda gwani na babbar Jam’iyyar mu mai gabatowa.

“Soyayyar Jam’iyyarmu ce ta sanya muka yanke shawarar ci gaba da zama a baya yayin da wasu ke fita duk da irin cin mutuncin da muke samu daga Jam’iyya mai mulki.

“Na yi alkawari zan yi muku hidima da himma, jajircewa da kuma duk abin da kuke so a zuciya da kuma masoyanmu.

“Dole ne mu hada karfi da karfe domin ceto al’ummarmu mai girma daga halin da take ciki a halin yanzu da jam’iyyar APC mai mulki ta sanya suka shiga.

“Kokarin da muke yi na hadin gwiwa ne wajen ganin an dora masu son tsayawa takara tare da tabbatar da gaskiya da kuma yabawa wadanda suka riga mu gidan gaskiya wajen yi wa jam’iyya da jama’a da kasa hidima.

“Ina neman kuri’un ku a zaben fidda gwani da za a yi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa,” inji shi.

Leave a Reply