An Yi Awon Gaba Da Wasu Jama’a A Ruwan Godiya Jihar Katsina

0
434

RUNDUNAR ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tana bincike kan rahoton sace gomman mutane a ƙauyen Ruwan Godiya a daren Litinin da ta gabata.

Bayanai sun ce maharan sun shiga ƙauyen na ƙaramar hukumar Faskari, inda suka sace mata da ƙananan yara sama da arba’in kafin su sako wasu daga bisani.

Katsina na cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Wani mazaunin garin Ruwan Godiya da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce da misalin karfe tara ne Ɓarayin suka afka musu, kuma akalla sun zo a kan babura sama da 30.

Ya kuma shaida cewa duk kuwa da cewa akwai sojoji a garin amma hakan bai hana su yin aika-aikar ba.

“Sun kwashe sama da mutane 40, ciki da mata da kananan yara da tsaffi, amma daga bisani suka dawo da wasu almajirai da suka kwasa. Barayin sun kasu kashi biyu, wasu na dibar mutane yayin da wasu ke harbe-harbe, babu wanda suka harba illa dai harbi a sama.

Amma sun rike sauran mutanen sama da 30, gidan mutum guda sun dauki mutum 13 ciki har da matan shi da ‘ya’ya, wanda a ko a bara na sace shi sai da aka biya naira miliyan 7 kafin suka sako shi.”

Mutumin ya yi zargin an san da zuwan ɓarayin, saboda wasu sun kira ta wayar tarho cewa ɓarayin na kan hanya, amma babu wani abu da aka yi.

Ya ce garuruwan da ke kewaye da su daga kan Ruwan Godiya, da Shema dukka akwai sojoji amma abin mamkin shi ne sai barayin su shigo hankali kwance su yi abin da suka ga dama su fita kalau ba tare da na yi musu komai ba.

BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah wanda ya shaida cewa suna gudanar da bincike kan wannan iƙirari.

Jihar Katsina dai na fama da matsalolin tsaro kama daga barayin daji, da masu satar mutane domin neman kudin fansa da sauransu.

Amma gwamnatin jihar na cewa ta na bakin kokari domin shawo kan matsalar, amma mazauna garuruwa da kauyuka na ci gaba da fuskantar tashin hankalin rashin sanin lokacin da ɓarayin za su afka musu ko kuma abin da zai faru idan sun kawo hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here