Labarin yana gefen ku!

Ƙabiliar Habasha, inda ake karrama maza masu ƙaton ciki da teɓa

1

Mutanen Bodi (ko Me’en) suna ɗaya daga cikin al’umomin da ke zaune a yankin Basin Omo-Turkana, a gabashin kogin Omo.

Bodi shine sunan da gwamnati ke kiransu da shi, amma mutanen Bodi suna kiran kansu Me’en. Me’en ƙabila ce mai ta al’umommi da yawa, kuma Bodi na daga cikinsu, yawansu ya kai kusan mutum 10,000.

A cikin mutanen Me’en, ana ɗaukar Bodi a matsayin mafi kusanci ga kakanninsu ta hanyar al’adasu ya yin kiwo. Shanun da waɗannan mutane ke kiwon na da matukar muhimmanci ga zamantakewa da tattalin arzikinsu.

Bodi na amfani da hadayar shanu a yawancin bukukuwan al’adunsu, suna bada shanu a matsayin sadakin aure ga matansu; Bugu da ƙari, shanu suna samar da isasshen abinci ga iyalansu.

Maza na ƙabilar Bodi suna gasa don kasancewa waɗanda suka fi ƙiba a ƙauyen ta hanyar shan jini da aka cakuɗa madarar shanu yayin da suke zaune a keɓe a wuri guda har tsawon watanni shida babu fita.

Maza daga ƙabilar Bodi suna gasa don zama masu ƙiba a sabuwar shekara ko bikin Ka’el, kuma watanni shida suke kwashewa suna shan hadakar jini da madara a ƙoƙarinsu na aijje teɓa da sauri.

Mutumin da ya ci nasara ba ya samun kyauta, ƙabilan na ba shi a matsayin gwarzo na rayuwa a cikin kabilar Bodi (Habasha), an fi son mazan da ke da ciki mafi girma, kuma mafi girman ciki, mafi ka kasance abu mai matuƙar kyau a al’adarsu.

Amma shirye-shiryen gasa inda ake zaɓar mafi ƙiba yana da ban tsoro, suna shan jinin saniya gauraye da madarar saniya na tsawon wata 3 zuwa 6 a ƙoƙarinsu na ajje teɓa da sauri ta yadda za su zamo masu ƙaton ciki.

A lokacin bikin Kael, ana auna wanda ya yi nasara a gasar kuma yana samun babban lambar girmamawa daga kabilar.

Mata da ‘yan mata suna kawo musu madarar da aga gauraya ta da jini a kowace safiya duk a ƙoƙarinsu na ajje teɓa.

Kyauta kawai ga wanda ya ci nasara shine shahara da kuma yabon ‘yan ƙabilarsa.

Mata suna kula da maza masu kiba: suna ba su barasa, suna share masu gumi, suna yi musu waƙa don su farka, daga barci.

Al’ummar Bodi na son ci gaba da riƙe al’adunsu amma suna fuskantar barazanar tsare-tsaren sake tsugunar dasu da gwamnati ke yunƙurin yi.

Abin baƙin ciki, al’adar Ka’el da al’adun gargajiya na Bodi na fuskantar barazana daga gwamnatin Habasha da ke shirin tsugunar da mutane 300,000 daga ko’ina cikin kasar.
A yanzu, ƙabilar na ci gaba kamar yadda suka saba kuma har yanzu suna bikin Ka’el a cikin salon gargajiya a kowa ne watan Yuni.

Leave A Reply

Your email address will not be published.