Zaben 2023: Dattijo Ya Yi Alkawarin Ci Gaba Da Ayyukan El-Rufai Idan Aka Zabe Shi

0
426

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A YAYIN da guguwar zaben ke kara karatowa domin zaben wanda zai maye gurbin Gwamna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i a gidan Sir Kashim Ibrahim Kaduna, wani dan takarar Jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Mohammed Sani Dattijo, ya kaddamar da wani shiri mai dauke da tsari shida yayin tsayawa takara a Jihar domin tunkarar babban zaben shekarar 2023.

Dattijo wanda ya jagoranci dimbin magoya bayansa zuwa Sakatariyar Jam’iyyar APC a ranar Talata, ya yi alkawarin ci gaba da kyawawan ayyukan da Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i ke yi idan aka zabe shi.

Dan takarar Gwamnan wanda ya kasance tsohon shugaban ma’aikata (CoS) ga Gwamna El-Rufa’i kuma kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare, ya nemi goyon bayan shugabannin Jam’iyyar gabanin zaben fidda gwani na Jam’iyyar domin fitowa a matsayin mai rike da tutar Jam’iyyar.

Jim kadan bayan kammala ganawar da shugabannin Jam’iyyar a sakatariyar APC na Jihar, Dattijo ya yi jawabi ga manema labarai inda ya fitar ajandarsa guda shida wanda idan aka zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar zai aiwatar.

A cewarsa, tsarin nasa su ne, “Tabbatar da ci gaba da gina Jihar Kaduna domin tabbatar da tsaro da saka hannun jari ga Jama’ar, kana da amfani da sabbin fasahohi don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen Jihar ta Kaduna.

“Samun canji na haɗa tattalin arzikin yankunan karkara zuwa Noma da Ƙarfafa samar da ma’adanai masu daraja domin samar da yanayi mai aminci da tsaro don bunƙasa rayuwa.

“Karfafa samar da Kayayyakin Gari domin Fadada Shirin Sabunta Birane na Kaduna domin mayar da Jihar wuri mai samar da damammakin tattalin arziki ga kowa.

“Gina Kaduna mafi kyau da ci gaban fasaha da daidaita tsarin mulki, yin amfani da fasaha don sanya Jihar Kaduna ta zama cikin tsara kuma shiri don tattalin arzikin kamfanoni masu zaman kansu.

“Saka hannun jari a cikin mutane – Samar da yanayi mai kyau kuma mai haɗaka ga jama’ar mu masu juriya ta hanyar zuba jari a kiwon lafiya, ilimi, ci gaban matasa da ayyukan yi.

“Jan hankalin abokan hulda na gida da na waje na kasa da kasa don samun Ci gaba. Yin aiki tare da abokan haɗin gwiwar ci gaba a duk faɗin duniya don ƙaddamar da nasarar ci gaba mai dorewa da kuma tabbatar da cewa ba a bar mafi yawan Jama’a a baya ba.

“Babban burina shi ne in mayar da Kaduna Jihar da za ta kasance mai tsaro, mai aiki ga kowa da kowa, samar da yanayi mai kyau na damammaki ta yadda dukkan mazaunanmu za su ci gaba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here