Bance Wani Yanki Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Ba – Gwamna Tambuwal

0
299

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

GWAMNAN Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya Karyata wani rahoton da ake danganta wa da shi cewa wai wani yanki ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba idan Jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takara daga yankin.

A cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai Muhammad Bello da aka rabawa manema labarai cewa hakika wannan rahoton ba gaskiya ba ne, an dai shirya shi ne kawai domin a karkatar da hankulan jama’a kawai.

Ga dai bayanin kamar hada; ” An jawo hankalin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya zuwa wani kanun labari na batanci a wani labarin da wata jarida ta rubuta, da yake cewa wani yanki a cikin kasar nan ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba”.

Leave a Reply