Za Mu Yi Kokarin Kare Rayukan Yan Najeriya Dake Ko’ina A Duniya – Hon Munir Lere

0
280

Daga; BASHIR BELLO, Majalisa Abuja.

DAN Majalisa mai wakiltar mazabar Lere ta Jihar Kaduna a Tarayyar Najeriya, Honarabul, Injiniya Ahmed Munir, ya ba da tabbacin cewa hakkinsu ne tabbatar da kare rayuka da lafiyar duk wasu yan Najeriya a duk fadin duniya, musamman a cikin irin wannan yanayin wanda wasu suka tsinci kansu na halin tashin hankali a kasar Rasha da Ukraine.

Injiniya Ahmed Munir a wata hirarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman tattaunawar Majalisar Inda suka mika wani kudirin neman mafita na gaugawa ga al’ummar Kasar da ke cikin wani halin ha’ula’i sakamakon rikicin daya barke a kasashen biyu na Rasha da Ukraine, ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Najeriya za ta kaiwa al’ummar dake zaune a kasashen dauki na gaugawa.

Ya kara da cewa, a bisa yunkurin da kudirin da suka gabatar yake na ganin cewa an samu mafita ga al’ummar da abun ya shafa, Majalisar Tarayyar ta amince da daukar matakai na gaugawa, kana da bada umarnin kwasho al’ummar da suke zauna a cikin kasashen biyu da lamarin ya shafa domin tabbatar da an kare lafiyarsu da rayuwarsu.

Ya ce “a matsayinmu na yan Majalisu, alkawarin da muka dauka shi ne ko’ina dan Najeriya yake za mu yi kokarin tabbatar da basa cikin wani hadari, don haka muna sane cewa akwai rikici na yaki dake faruwa tsakanin Kasar Rasha da Ukraine a yanzu haka, saboda haka ya zama wajibi mu kare rayuka da lafiyar yan Kasarmu a duk inda suke.”

“Bayan haka ma, ana sane cewa muna da dalibai da dama daga ko’ina a fadin Tarayyar Najeriya da suke karatun Koyon aikin likitanci da sauran darussa da suke chan Kasashen, saboda haka wajibi ne a kare lafiyarsu ta hanyar samun yadda za a fitar da su daga cikin wannan hadarin da suke fuskanta wanda hakan yasa muka gabatar da wannan kudirin a yau.”

“Sai kuma abu na biyu na aikin dake gabanmu shi ne ba wai yin bayanin ne kawai ba face daukar matakin gaugawa wanda hakan yasa kakakin Majalisar ya kara bada tabbaci akai domin a samu Jiragen da za su je su kwaso wadannan mutanen da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayyar ta hanyar hukumar harkokin kasashen waje da ya zama wajibi su kula da duk wasu harkokin.”- Inji Shi

Acewarsa, duk wasu ka’idodin da matakan da ya kamaci Majalisar ta bi ko ta dauka domin tabbatar an aiwatar aikin da duk hanyoyin da za a bi domin a samu damar tsaratar da al’ummar Kasar Najeriyan dake kasashen biyu, a yanzu sun riga sun kammala wannan shirin, face illa Gwamnatin Tarayyar kadai suke jira domin ta bada umarnin fara aiwatar da ayyukan domin a kwaso al’ummar.

Har’ila yau, Dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar mazabar Lere, ya kara da bada tabbacin cewa baya ga Kokarin ganin an tseratar da al’ummar da ke kasashen, Majalisar za ta yi duba a kan al’amuran da suka shafi sakala daliban da harkokin karatun su zai tsaya a wasu wajajen da suka dace sakamakon matsalar da aka samu don ganin cewa karatunsu bai tsaya ba bayan kwaso su da za ayi.

Daga karshe, Honarabul, Injiniya Ahmed Munir, ya shawarci yan Najeriya dake da yan Uwa a kasashen da abun ya shafa da su kwantar da hankalinsu, kana su ci gaba da yin addu’a domin ganin cewa an samu cin nasarar tsaratar da duka al’ummar Kasar dake kasashen biyu.

Leave a Reply