Yaron gida ya faɗi, ya mutu, bayan uwargidansa ta tilasta shi ya yi lalata da ita

0
83

Daga Maryam Umar Abdullahi

A al’ummar Akinjagunla da ke jihar Ondo, wani yaron gida Abiodun Akintomowo ya gamu da ajalinsa bayan uwargidansa, ta tilasta shi ya yi jima’i da ita, mai suna Bimpe. Lamarin ya faru ne a wani fitaccen gidan hutawa da ke ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma.

Bayan kammala jima’in, nan take Akintomowo ya yanki jiki ya faɗi ya rasu. Uwargidansa, matar wani mai gidansa, sai tayi kururuwa kuma ta faɗi ta suma, amma ba ta daɗe ba ta farfaɗo. Majiyoyi sun bayyana cewa an kai gawar marigayin zuwa ɗakin ajiye gawawwaki na jami’ar kimiyar lafiya da ke garin Ondo.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wata majiya ta nuna cewa, wannan bala’in na da nasaba da yadda aka yi wa uwargidan tsawa da aka yi mata laƙabi da “Magun”. Kamar yadda shaidu suka bayyana, matar ta ɗaga murya ne bayan ta fahimci faɗuwar Akintomowo. Manajan otal ɗin da mazauna garin sun garzaya wurin da lamarin ya faru, a ƙoƙarin ceto shi, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

KU KUMA KARANTA: Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Hukumar kula da masauƙin baƙi ta kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda na yankin Yaba da ke unguwar, lamarin da ya kai ga ɗaukar gawar marigayin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Fumilayo Odunlami-Omisanya, ya bayyana cewa tuni aka kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin mutuwar Akintomowo.

Leave a Reply