‘Yan sandan Legas sun kama wasu da ake zargi da ɓarnata titin jirgin kasa

2
395

Tawagar ‘yan sintiri daga sashin ‘yan sanda na Ijora Badiya sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da lalata titin jirgin ƙasa a jihar Legas.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA:Harin Jirgin kasa: NAWOJ, Ta Yi Allah-Wadai Da Kakkausar Muryar Bisa Mummunar Ta’addancin

Ya ce, “da misalin karfe 1 na safiyar yau, tawagar ‘yan sintiri daga sashin Ijora Badia sun tare wata mota kirar Mitsubishi Lancer dake ɗauke da kayan titin jirgin kasa da suka lalace.

“An kama mutanen biyu dake cikin motar. Ana ci gaba da bincike.” inji shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply