Ƙungiyar Arewa ta nemi a binciki kisan da aka yiwa Fulani makiyaya a Nasarawa

0
450

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta bincike kan halin da ake ciki dangane da kisan da aka yi wa Fulani makiyaya da mahauta 40 a kusa da garin Doma na jihar Nasarawa, wanda ake zargi wani jirgi mara matuki da kai harin a ranar 25 ga watan Janairun, 2023.

Rahotanni sun nuna yadda aka kashe makiyaya a ƙauyen Rukuni da ke karamar hukumar Doma a Nasarawa a makon jiya.

An ce masu gadin sun bi sawun makiyayan tare da kashe su a lokacin da suke sauke shanun jim kaɗan da isa inda suke a Nasarawa.

KU KUMA KARANTA:A gabana ‘yan sanda suka kashe makiyaya, bayan Abba Kyari ya nemi in ɗorawa Saraki laifin fashi – Ɗan fashi ga Kotu

Sai dai kungiyar ACF a lokacin da take mayar da martani kan kisan, ta bakin babban sakatarenta, Murtala Aliyu a jiya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan ɗanyen su kuma fuskanci doka.

A cewar sanarwar, “ACF tana kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa makiyaya da mahauta sama da 50 a kusa da Doma, jihar Nasarawa a sakamakon luguden wuta da jiragen suka yi a ranar 25 ga watan Janairun 2023.

“A saninmu gwamnati ce kawai ke da ikon tura jirage marasa matuka, halin da ake ciki na kashe makiyaya da suka je Makurdi, babban birnin jihar Benue domin kwato shanu 1250 da aka kama daga hannun masu gadin Dabbobin Benue bayan biyan tarar Naira miliyan 29 ga masu gadi.

Majiyar ta shaida wa ACF cewa harin da jiragen yaƙi mara matuki ya faru a lokacin da ake kwashe dabbobin bayan an tilasta musu kwashe shanun su a cikin manyan motoci daga Makurdi.

Wannan lamari dai ya zo ne bayan watanni shida da kashe ɗaruruwan dabbobi a lokacin da wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojojin saman Najeriya daga rundunar Operation Base ta Makurdi ya kai wani samame tare da kashe da raunata dabbobi da kuma wasu makiyaya a garin Awe da ke jihar Nasarawa.

Ya ce a wata ƙasa mai tsanani, mutuwar mutum ɗaya ya isa ya jawo hankali da kuma tsoma bakin gwamnati, ya kara da cewa, “Gwamnatin Tarayya ce ke kula da sararin samaniyar Najeriya ta hannun Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA).

“Don haka muna sa ran Gwamnatin Tarayya ta gaggauta zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin, domin su fuskanci shari’a.”

Ya yabawa gwamnatin Nasarawa bisa irin gudunmawar da ta yi kawo yanzu wajen ba da kulawar lafiya da tallafawa wadanda suka tsira da rayukansu da kuma iyalan wadanda abin ya shafa.

Yayin da ya ke yin Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin “ƙisan da bai dace ba”, ya jajantawa ACF ga iyalan wadanda suka mutu da kuma gwamnatin Nasarawa tare da yin kira da a biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply