Connect with us

Labari

‘Yan Sanda Sun Kama Masu Ci Da Sayar Da Naman Mutane A Zamfara

Published

on

Bello Matawalle

Daga Rabo Haladu

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Zamfara ta kama mutum hudu da zargin ci da kuma sayar da sassan jikin dan adam, wani abu da ba a saba gani ba a jihar.

A taron manema labarai da ya gudanar a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara ranar Alhamis, Kwamishinan ‘yan sanda Ayuba Elkana ya ce an damke wadanda ake zargin ne bayan da jami’an tsaro suka tsinci gawa a wani kango, ba tare da wasu sassan jikinta ba.

Gano gawar wani bangare ne na bincike da ake yi kan batan wani yaro dan shekara tara.

Tun a makon da ya gabata aka ma mutanen hudu da a ke zargi, da suka hada da wasu magidanta maza biyu da kuma matasa suma maza biyu kamar yadda CP Elkana ya sanar.Ya kara da cewa yanzu haka ana kan neman wasu mambobin kungiyar da ake zargi da cin naman mutane.Kazalika kwamishinan ‘yan sandan ya ce kawo yanzu bincike ya nuna cewa sau biyu shugaban kungiyar na tura wa uku daga cikin wadanda aka kama naira 500,000 na cinikin sassan jikin dan adam.Cin nama da sayar da sassan jikin mutane wani sabon abu ne a Zamfara, duk da jihar ta yi kaurin suna wurin kashe-kashe da garkuwa da mutane don neman kudin fansa daga ‘yan bindiga tsawon shekaru.

Kuma hukumomin Najeriya na shan suka saboda nuna gazawa wurin shawo kan halin da jihar ke ciki.

A wata mai kama da haka yayin zantawa da manema labaran CP Ayuba Elkana ya ce jam’ian tsaro sun kubutar da mutun 17 da aka sato daga jihar Neja aka shiga da su Zamfara.

Ya kara da cewa yayin wani sintiri, ‘yan sanda sun kwato makamai da suka hada da bindigar harba makamin roka, bayan bata kashi da ‘yan bindiga a wani daji da ke yankin.

A makon da ya gabata ne ‘yan fashin daji suka kashe kusan mutun 200, a lokacin da suka kai wasu jerin hare-hare a kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labari

EMAS69 • LINK ALTERNATIF SPORTBOOK SBOBET

Published

on

By

Emas69 adalah bandar taruhan sportbook sbobet terlengkap yang saat ini sangat dikenal seluruh masyarakat Indonesia dengan melalui link alternatif Emas69. Pada permainan taruhan sportbook, setiap pertandingan sepak bola yang dilangsungkan dapat dijadikan sebagai tempat bagi seluruh masyarakat Indonesia untuk melakukan taruhan dengan menggunakan uang asli. permainan taruhan bola online dapat dilakukan dengan bebas sesuai dengan pertandingan yang berlangsung dan juga team sepak bola yang disenangi untuk memperoleh kemenangan dan kepuasan dari setiap taruhan sportbook di situs Emas69.

Continue Reading

Labari

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Published

on

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi - TUC/NLC

Albashi mafi ƙaranci: Da babu gara ba daɗi – TUC/NLC

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.

Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.

KU KUMA KARANTA:NLC ta ƙira taron gaggawa bayan gwamnati ta jingine batun ƙarin albashi

Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Najeriya Naira 615,00 ya sauƙo Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.

Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadagon ta TUC Komared Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar ƙolinmu, tayin da shugaban ƙasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 ɗin nan da babu ne gara ba daɗi.

Tuni ma’aikata na sassa daban-daban suka fara maida martani da mafi sauƙin shi ne na nuna ba abun da suka iya don jagorori sun miƙa wuya.

Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.

Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Najeriya matuƙar gwamnati ba ta farka ta ɗauki matakan gaskiya na zahiri ba.”

Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ‘yan ƙwadagon sun yaɗa gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.

Continue Reading

Kasashen Waje

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Published

on

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump - Pennsylvania

Mun yi wa shugaba Biden bayani kan harbin da aka yi wa Trump – Pennsylvania

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yaƙin neman zaɓen tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, “Ni da Daraktan ma’aikatar leƙen asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma’aikatar Leƙen Asiri suna aiki tare da abokan aikinmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

KU KUMA KARANTA:Kotun Ƙolin Amurka za ta yanke hukunci kan takarar Donald Trump

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leƙen asiri bisa matakin gaggawar da ta ɗauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yaƙin neman zaɓensu, kuma muna ɗaukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban ƙasa da kuma taron yaƙin neman zaɓensu na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifik

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leƙen asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI.”

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like