‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Kwalejin Mata A Jihar Zamfara

0
771

Daga; Rabo Haladu.

WASU ‘Yan bindiga sun sace ɗaliban Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya mata huɗu a ranar Talata da daddare a Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin ya faɗa cewa maharan sun afka wa gidan da ɗaliban ke zaune wanda ke wajen makarantar a garin Tsafe bayan sun tarar da jami’an tsaro na gadin kwalejin.

Shugagan kwalejin, Yusuf Idris Maradun, ya ce ɗalibai biyar ‘yan bindigar suka kama amma daga baya suka saki ɗaya daga cikinsu saboda ta kasa tafiya sakamakon lalurar ƙafa.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ce jami’an tsaro sun duƙufa domin ganin an ceto ɗaliban da aka sace a gidan da suka kama haya suna kwana a cikin garin na Tsafe.

Leave a Reply