‘Yan bindiga sun kashe malami a harin makarantar Nasarawa

0
274

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Rahotanni sun ce an kashe wani malami mai suna Mista Auta Nasela bayan wani hari da aka kai makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) Nasarawa-Eggon, Jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Asabar.

Wani ma’aikacin makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata cewa ‘yan bindigar sun shiga harabar makarantar ne kai tsaye suka nufi gidan marigayin suna neman kudi.

Marigayin ya garzaya zuwa gidan makwabcinsa, amma daya daga cikin ‘yan bindigar ya bindige shi ya harbe shi, a cewar majiyar.

Ya ce an harbe wani ma’aikacin makarantar Mista Timothy Malle, amma ya tsallake rijiya da baya, inda ya ce an garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce lamarin na fashi da makami ne.

“A jiya, da misalin karfe 8:45 na dare, an samu kira daga GSS Nasarawa-Eggon cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan wani Auta Nasela.

“Lokacin da suka shiga, sai suka fara neman kudi amma mutumin da ya tsere zuwa gidan makwabcinsa, amma daya daga cikin maharan ya bi shi ya harbe shi.

Nansel ya kara da cewa “‘yan sanda sun garzaya da shi babban asibitin Nassarawa-Eggon, amma abin takaici, ya mutu ne a lokacin da yake karbar magani.”

PPRO ya ce tun daga lokacin ne rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike a kan lamarin da nufin cafke su tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Ya yi kira ga jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda bayanai game da masu aikata laifuka domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply