‘Yan bindiga sun kashe ɗan Majalisar PDP na Adamawa

0
327

Daga Fatima GIMBA, Abuja

A safiyar ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka kashe mataimakin shugaban majalisar dokokin Ƙaramar pp 0′ hukumar Song ta jihar Adamawa, Hon. Ishaya Bakano.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin gidansa da ke Bannga da sanyin safiyar Asabar, inda suka kashe shi kuma suka fice nan take.

An yi imanin cewa an kashe Ishaya ne bisa manufa na kisa.

A cewar wata majiya daga iyalansa, ‘yan bindigar sun kuma harbe dansa wanda yanzu haka yake jinya a asibitin Song.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar, kuma jami’an tsaro na bakin ƙoƙarin su wajen cafke wadanda ake zargin.

Leave a Reply