‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano

0
1566

Jami’an ‘yan banga sun kama wani baƙo (an sakaya sunansa) bisa zargin yunƙurin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 9 mai suna Fauziyya Muhammad a unguwar Darmanawa da ke ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, iyayen Fauziyya tare da ’yan’uwanta mata biyu ne iyayensu suka aiko su sauke wani fim a wata cibiyar sadarwa da ke kusa da su, sai mutumin ya bi ’yan matan tare da yi musu alƙawarin ba su kayan wasan yara idan suka bi shi zuwa wani wuri.

KU KUMA KARANTA: Masu ƙwacen waya sun yi yunƙurin hallaka ɗan Jarida a Kano

“Yan uwanta sun dawo gida suna kuka, suka ce wani ya ja ‘yar’uwarsu wani wuri da ya yi mata alƙawarin zai ba ta abin wasa. Mun sanar da mutane, inda suka bi shi zuwa maƙabarta a nan ne suka kama shi,” inji mahaifiyarta.

A halin da ake ciki, wanda ake zargin ya ce ba wai yana ƙoƙarin sace yarinyar ba ne, sai dai ya ƙwace wayarta ne, ya ƙara da cewa ya yi alƙawarin ba ta wani abin wasa.

Wanda ake zargin ya amsa cewa, “Ina so ne na karɓi wayar da take riƙe da ita, shi ya sa na nemi ‘yan’uwanta su jira. Kafin ma na karɓi wayar mutane sun gano ni sun kama ni.”

Jami’an ‘yan banga da kwamatin al’ummar sun ce za su miƙa shi ga ‘yan sanda bayan kammala taro da bincike. Kano dai na fama da ayyukan sace-sacen waya a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya sa wasu ke ta ƙiraye-ƙirayen a ayyana ‘yan fashi da makami. Shugaban masu siyar da waya a Kano Ashiru Yusuf Yakasai ya ce, “Muna da shari’o’in da ake yanke wa masu satar waya hukuncin a matsayin ƙananan laifuka.

Za su je gidan yari su dawo su ci gaba da abin da suke yi, duk da cewa suna ɗauke da muggan makamai har ma da jikkata mutane.

“Hanya ɗaya tilo ita ce majalisar dokokin jihar da duk masu ruwa da tsaki su bayyana su a matsayin ‘yan fashi da makami”.

Leave a Reply