Yadda wata mata ta tunkuɗo ‘yar aikinta daga bene a Anambra

0
338

Labari daga Fatima Abubakar MONJA, Abuja

Yan sandan jihar Anambra reshen Anambra ta gabas suka kama wata mata mai suna Owanna Nnanna yar shekara 29 a duniya bisa laifin yunƙurin kisan kai a ranar asabar 2 ga watan yuli a titin Otu, dake Awada Onitsha.

Da ake zantawa da da kakakin ‘yan sanda, ya tabbatar da lamarin yace an kama wacce ake zargin tare da tsare ta, yayin ‘yar aikin da aka cillo cikin ikon Allah bata mutu ba, take ci gaba da karbar kulawa a asibiti.

A cewar mai magana da yayun rundunar ‘yan sanda DSP Ikenga Tuchikwu, binciken farko ya nuna wacce abin ya shafa Ijeoma Nwafor yar shekara 14, kuma ‘yar asalin garin Achalla da ke Anambra ta Gabas, ana zargin matar ta turata ne daga wani bene mai hawa hudu a lokacin da take dukanta.

Tochukwu ya kara da cewa wacce aka cillo din ‘yar aiki ce a gidan wacce ake zargi.

Kakakin ya ƙara da cewa anyi caraf da wacce ake zargi, yayin da wacce aka cillo taje ci gaba da karban kulawa daga wajen likitoci.

Leave a Reply