YA RATAYE KANSA A JIGAWA

0
384

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI Da RABO HALADU

Wani dan shekaru 25 mai suna Naziru Badamasi, da ke zaune a kauyen Tsadawa cikin karamar hukumar Taura ya rataye kansa a jikin wata Bishiya, sakamakom hakan ya mutu har lahira.

Rundunar yan Sanda ta kasa reshen  Jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunsu ASP Lawan Shiisu, ya kuma tabbatar da faruwar hakan ne a ranar Talata a garin Dutse hedikwatar Jihar.

Inda ya ce marigayin ya yi amfani da Wandonsa ne ya kuma rataye kansa a jikin wani itace a ranar Litinin.

Ya ci gaba da bayanin cewa, Naziru Badamasi, mai shekaru 25 tun da farko an kawo masu rahotan cewa ba a ganshi ba, sai daga baya aka same shi ya rataye kansa a itace cikin daji a kusa da wani kauye mai suna Zangon Maje.

Ya bayyana cewa a ranar 24 ga watan Janairu da misalin karfe 2: 30 Hakimin Kwalam, Alhaji Muttaka Uba, ya kira waya inda ya ce wani Naziru Badamasi, a Kauyen Tsadawa karamar hukumar Taura, wanda ke fama da tabin hankali an neme shi ba a fan shi ba, bayan ya bar gida a wannan ranar da misalin karfe 12: 30 na Dare.

“Amma daga baya an gan shi bayan ya rataye kansa da Wandonsa a kan wata itaciya a can wani kauye Zangon Maje a karamar hukumar Taura”.

ASP. Shiisu ya kara da cewa bayan da aka samu wannan bayanin ne, wata tawagar jami’an Yan Sanda suka tafi wajen da abin ya faru sun kuma dauki Gawar zuwa babban asibitin Ringim, inda Likita ya tabbatar cewa hakika ya rasu.

Kamar yadda ya ce daga baya kuma aka mikawa yan uwan mamacin Gawar domin yi masa Jana’iza, kuma bayan gudanar da binciken farko a samu kowa da zargin hannu a game da faruwar lamarin ba.

Leave a Reply