Connect with us

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Woodaabe: Ƙabilar da mace ke kwanciya da maza birjik don haifan kyawawan yara

Published

on

Daga Fatima MONJA, Abuja

Ƙabilar Wodaabe ko Baroro yadda aka fi sanin su, ƙabila ne da suka yadda da rauhanai/aljanu amma sukan kira sunan Allah in suka ji wuya ko suka zo mutuwa.

Shafe jiki da jan yambu, shafe leɓe da baƙi

A al-adar su, mace ke da hurumin zaba ma kanta miji ko da kuwa tana da wani auren, kuma ta kwanta da su dukkan su ta haifa musu ‘ya’ya.

Suna da wata al’ada ta shafe dukkanin jikin su da Jan yunbu hakan ke bawa idanun su daman fitowa farare tass.

Kamar yadda jami’ar IOWA na ƙasar Amurka ta wallafa, ƙabilar Bororo sananniyar ƙabila ce wanda galibi ake samun su a arewacin Kamaru, Chadi, Nijar, da arewa masu gabashin Najeriya.

Wankan jan hankalin mata don su zaɓesu a bikin Gerewol

Yaɗuwar su a yankin kudu da sahara ya ba da gudunmawa ga rukunoni fiye da15. Mutanen ƙabilar sun yadu bisa auratayya tsakanin su da kuma tafiya da suke a ayari.

A ƙiyasi, ƙabilar Wodaabe sun kai 160,000 zuwa 200,000 sun kuma rarrabu ƙungiyoyi daban daban. Bororo na taruwa waje guda domin suyi raye rayen al’adan su na Geerewol, Worso da Yakke.

Ƙabilar Wodaabe na da ilimi sosai sai dai sun yadda da ajanu Rauhanai iri iri wanda suke rayuwa a bishiya da tsoffin rijiyoyi, sai dai in sunji wuya sukan kira sunan Allah ko in sukazo mutuwa.

Al’adun Boro na ban mamaki yayin bikin aure, yana zuwa a yanayin da ba’asaba ba. Wannan bikin al’ada ana kiran shi da Yakke, maza na taruwa tare da shafe jikin su da jan yunbu da gashin ido mai kauri dan bayyana fararen idanuwan su da yi baƙin baki don fararen haƙoron su a fuskokin su dan jan hankalin amaren su.

Bikin Gerewol

A lokacin akan jefa mutum cikin dutse tsawon awa shida ana gyara shi dan wannan lokacin, ai ta rawa a da’ira don jan hankalin ‘yan matan. A nan ne matan ke zaban gwani ko wanda yai nasara.

Mace na da ‘yanci zaban miji sama da daya, galibi a al’adan woodeeba maza basu da ‘yanci ko kadan wajen batun jima’i ko na hadin aure. Iyaye ke zabar mijin farko daga baya mace zata iya ƙarawa a lokacin bikin Gerewol. Abinda suke kira da “Sigisbesim.”

Taron zaɓen miji

Idan Amarya ta samu juna biyu to haramun ne miji ya ganta, tattarawa take ta koma gidan iyayenta har sai ta haife suna kiran hakan da “boofeydo” wanda hakan na nufin ya yi kuskure. A wannan lokacin ba abinda zai ƙara shiga tsakanin miji da matar sa sai bayan shera 2 ko 3, mijin zai samu wannan daman ne a lokacin da mahaifiyyar ta tagama shirya mata komai na komawa gidan shi.

Kasancewar ana girmama masu kyau a kabilar bororo hakan yaba mata daman suyi kwanciya da duk wanda ya mata, mijin ta ba yadda zaiyi koda kuwa ya gani. Idan miji yasan bashi da kyau, to zai iya ba wa matar shi dama taje ta kwanta da wanda yake da kyau dan ta haifi kyawawan yara.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Tsananin azaba ta sa wani ɗan Indiya rama cizon maciji

Published

on

Tsananin azaba ta sa wani ɗan Indiya rama cizon maciji

Tsananin azaba ta sa wani ɗan Indiya rama cizon maciji

Wani Ba’indiye mai suna Santosh Lohar ya gantsarawa wani maciji cizo har lahira a matsayin ramuwar gayya bayan da Maciji ya cije shi yana tsaka da bacci .

Santosh ɗan shekaru 35 daga garin Pandua, Jharkhand a Indiya, yana tsaka da barci wani Maciji ya rarrafo ya gasa masa cizo, nan take kuwa Santosh ya damƙo maciji da sanda inda shima ya gasa masa cizo.

Lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya ciji macijin, Lohar ya gaya bayyana cewa: ‘A ƙauyen mu mun yadda cewa idan Maciji ya cije ka to ka kama shi ka cije shi sau biyu don kashe dafin”.

Ya ƙara da cewa rama cizon da yayi shi ne ya hana shi mutuwa, kasancewar hakan wani canfine da sukayi imani da shi a yankin su.

READ ALSO: Maciji mafi dafi na biyu a duniya, ya ciji budurwa tana tsakar barci a gadonta

Duk da da ba a gama gane wane irin Maciji ne ya sari Lohar ba. Ba a tsaya ba aka garzaya da shi asibiti da ke kusa da su inda aka ba shi maganin kashe dafin aka sallame shi washegari.

Continue Reading

Allah Ɗaya Gari Bam Bam

Na yi yunƙurin yin azumi irin na musulmai, na kusa mutuwa – Wata Kirista

Published

on

Wata matar aure mai suna Eniola Fagbemi Sisialagbo ta bayyana cewa ita Kirista ce, amma mijinta Musulmi ne, kuma tana sha’awar yadda musulmi ke azumi, domin kullum sai ta tashi lokacin sahur, ƙarfe 4:30am domin shirya wa mijin nata abincin da zai yi sahur, hakan ne ya sa ita ma wata rana ta ce za ta jaraba azumin.

Ta ce bayan ta yi sahur gari ya waye, “ƙarfe 10 na safe sai cikina ya fara amsawa, amma duk da haka na dage har zuwa ƙarfe 12 sai naga idanuna sun fara jujjuyawa, nan na ɗauki waya na ƙira mijina na sanar masa halin da nake ciki, ya ce na daure, ko da ƙarfe huɗu ta yi na suma sau biyu, sai ganin kai na na yi a asibitin SAANU da ke garin Makola a Ibadan, jihar Oyo, na rantse da Allah wannan azumi da Musulmi ke yi ba wasa ba ne, ina jinjinawa Musulmi masu Azumi.” In ji ta.

Me yasa kuke ganin ta ka sa yin azumin?

Continue Reading

Al'ajabi

Bishiyoyin da ke zubar da jini: Yadda kimiyya da gargajiya suka yarda su raba hanya

Published

on

Daga cikin abubuwa masu ban a’ajibi a hallittun tsirrai, shi ne wata bishiyar fure da aka bai wa sunan “Zuciya mai zubar da jini,” wadda ake amfani da kyawunta wajen bayyana yanayin halayyar ɗan’adam da ba a buƙata.

A yayin da wannan bishiya ba ta zubar da jini a zahiri, hotuna da bidiyo a faɗin duniya na nuna yadda wasu bishiyoyi suke fitar da wani jan ruwa kamar jini, abun da ke ci gaba da tayar da hazo kan fassararsa a gargajiyance da kimiyyance a tsakanin al’ummu.

A yankuna irin su Kudancin Amurka, ana kuskuren kallon wannan ruwa a matsayin jini, yayin da a Afirka, abin da aka fi imani da shi shi ne wai wasu mutanen ɓoye ne da ke rayuwa a cikin bishiyoyin ke fitar da jan ruwan.

A watan Oktoban 2017, masanin tsirrai ɗan ƙasar Faransa ya bayar da haske kan yadda Tepezcohuite ko “bishiya mai aman jini”, ta zama abar girmamawa a wajen jama’ar Mayas da ke kudanci Mexico zuwa Guatemala.

Wani bidiyo da aka yaɗa a yanar gizo ya tabbatar da wanzuwar irin waɗannan bishiyoyi masu zubar da ruwa kamar jini. Mene ne abin da ake muhawara a kai game da wannan jan ruwa da ke bulbulowa?

KU KUMA KARANTA: Abubuwan al’ajabi da ke tattare da dabbar ‘Batoyi’ (Hotuna)

Kimiyya ta yi watsi da wannan abi bisa cewa camfi ne kawai idan aka ce wai wannan ruwa d abishiyun ke fitarwa jini ne. Amma jama’ar Shaman da masu bin addinan gargajiya na yi wa wadannan bishiyu kallon masu tsarki.

Dr Djibril Diop, masanin muhalli kuma malami a Jami’ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar babban birnin Senegal, ya bayyana cewa babu wata bishiya da ke aman jini ko take da wani ikon amfanarwa ko cutarwa saboda jan ruwan da take da fitarwa.

Ya nanata cewa wannan ruwa wani ɗanko ne ko ruwan cikin tsirrai danda ke taka muhimmiyar rawa wajen rayuwarsu.

Ɗankon cikin tsirrai wani ruwa ne da ke fita daga bishiya don tsaron kanta, inda ruwan cikin jijiyoyin bishiya kuma yake kasancewa fari, kuma yana fita da tsakanin gajye da reshe, wanda shi ke kai ruwa, gishiri, ko sukari ga tsirrai.

Dr Diop ya bayar da misali da bishiyar darbejiya a yankin Bandafassi take fitar da wani farin ruwa mai yawa saboda harin ciwon fungal.

“Mazauna yankin na fassara wannan da wani abin a’ajibi kan bishiyar, ba tare da sun san cewa yanayin bishiyar, yankin da take, ƙasar data fito daga ciki da kuma yanayin ciwon da za ta yi na taka rawa wajen fitar ruwan da kalarsa.

Masanin muhallin ya kuma yi nuni da cewa babu wata bishiya da ke da jini, a saboda haka a hankalce, ba za a taɓa tsammanin ta fitar da jini ba.

Ya bayar da misali da bishiyar da ake ƙira Socotra don nuni ga yadda ɗanko a reshan bishiya yake, tare da kalar jan da wasu ke tunanin ko jini ne.

Wannan bishiya da za ta iya tsayin har mita 20, na fitar da ruwa ja daya sanya har aka rubuta wasu makalolin kimiyya don bayyana ta a matsayin “bishiya mai aman jini”.

Wannan jan ruwa ya haɗa da sukari, ruwa da wasu sinadaran gina jiki, kuma a wasu al’adu ana amfani da shi wajen rini. Ana yawan alaƙanta wannan ruwa ja ga ƙarfin tace sinadarai da bishiya ke yi.

Baya ga amfani da su wajen yin rini, masana tsirrai irin su Dr Diop da masu maganin gargajiya irin su Romaric Moussounde Moussounda na da ra’ayin cewa wadannan bishiyoyi na yin magani.

Moussounda, wanda ke da fahimta kan bambance-bambancen dazukan Gabon, na da ra’ayin cewa halittu da yawa, ko nau’ikan bishiyoyi Pterocarpusda ke Afirka ko na Abitibi da ke Quebec, duk sun cancanci a yi musu kallon masu matsayi na musamman ko yin camfi game da su.

Moussounda ya na cewa “Waɗannan bishiyoyi kyauta ce daga Ubangiji da bai kamata su faɗa wani rukunin rashin tabbas ba.”

“Wannan ruwa da ke fitowa daga cikin waɗannan bishiyoyi na jini ba ne, amma kuma na da muhimmanci da matsayi irin na jini.”

Moussounda wanda ke cakuɗa gargajiyanci da zamananci a fannin kula da lafiyar zuciya da sauran ayyukan gaggawa na kula da lafiya, ya rawaito marubuci dan asalin Senegal Birago Diop, wanda a 1960 ya yi rubutu game da “Tsarkin wasu bishiyoyi”.

Moussounda ya ce “Ana yawan amfani da waɗannan bishiyu masu tsarki wajen bukukuwa da magani. Duk suna da wata alaƙa ruhaniyya ga ɗan adam.”

A yayin da masana tsirrai ke ta fashin baki kan waɗannan bishiyu masu aman jini, su kuma mabiya addinan gargajiya irin su Mayan da ke Mexico da ‘yan asalin Indiya na Barazil ko Kudancin Amurka na da ra’ayin lallai a kalli waɗannan bishiyoyi a matsayin masu tsarki ababan girmamawa.

Duk da waɗannan bambance-bambance na ra’ayi, akwai ijma’i tsakanin masana kan lallai a kare wadannan bishiyoyi, ko suna da tsarki ko babu, don kare muhalli.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like