Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe

0
75
Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe
Mai laifi

Wani uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 8 fyaɗe

Wani mai sayar da maganin gargajiya ya gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da yi wa ɗiyarsa mai shekaru takwas fyaɗe.

An gurfanar da magidancin mai shekaru 35 a kan tuhume-tuhume guda na fyaɗe, wanda rundunar ‘yan sandan ta ce ya saba wa sashe na 25 (a) na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Ondo ta shekarar 2021.

Dan sanda mai shigar da ƙara, Sufeto Martins Olowofeso, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake ƙara ne a ranar 18 ga watan Yuni, 2024 bayan rahoton da aka kai ga sashin yaki da garkuwa da mutane na ’yan sanda a Alagbaka, cewa ya yi wa ’yarsa fyaɗe.

Daga bisani an tsare wanda ake tuhuma don ci gaba da bincike.

A cewar Mista Olowofeso, wanda ake zargin tare da matarsa ​​sun gudu daga gidansu bayan aikata laifin inda suka je Jihar Osun suka samo rahoton likita na ƙarya, da ke nuna babu wani abu da ya samu yarinyar.

Ya kuma shaida wa kotun cewa jami’in bincike na ’yan sanda ya sake yin wani gwaji a Akure, wanda ya nuna cewa an zakke wa yarinyar, kuma ta kwashe kwanaki uku tana zubar da jini.

A cewar Olowofeso, wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake zargin sa da shi a lokacin da jami’in da ke binciken ya yi amsa tambayoyi.

KU KUMA KARANTA: An ɗaure ɗan shekara 17 shekaru 14 a kurkuku saboda fyaɗe

Olowofeso ya buƙaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Olokuta har zuwa lokacin da za ta samu da shawara daga sashen shigar da kara na gwamnati (DPP).

Lauyan wanda ake ƙara, G.O Omoedu, ya shaida wa kotun cewa an kai wa wanda yake karewa sammaci ƙurarren lokaci kuma zai buƙaci lokaci domin ya mayar da martani kan batun shari’a.

Ya buƙaci kotun da ta dage ci gaba da shari’ar don ba shi damar amsa buƙatar ci gaba da sauraren ƙarar.

Majistare B.A. Alipohul ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙara a hannun ’yan sanda sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Yulin 2024.