Uba Sani Ya Bada Tallafin Kayan Agaji Ga Al’ummar Giwa, Kaura Na Miliyoyin Naira

0
375

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SANATA Uba Sani mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayar da kayan agaji da tallafi ga al’ummar da rikicin ‘yan bindiga ya shafa a karamar hukumar Giwa da Kaura.

A wani sakon dake dauke da sa hannun Abubakar Rabi’u Abubakar, Shugaban mazabar Shiyya na Sanatan a ranar Alhamis din da ta gabata, ya bayyana cewa Dan takarar Gwamnan ta Jihar Kaduna karkashin Jam’iyyar APC, ya bayar da tallafin ne biyo bayan halin kuncin da al’ummar suka tsinci kansu a yankunan a yan kwanakin nan.

Ya kara da cewa, Sanatan ya jajantawa al’ummar da abin ya shafa a wadannan al’ummomi tare da addu’ar Allah ya ba su ikon jure radadin rashin wadanda suka rasa rayukansu.

Ya ce “Idan za a iya tunawa dai, Sanatan a zauren majalisar dattawan, ya bayar da shawarar matakin da zai bai wa jami’an soji damar gudanar da ayyuka ba tare da tangarda ba, wajen shafe masu aikata laifuka a yankunansu.”

“Sanatan ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da hare-haren da ake kaiwa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba da asarar dukiyoyinsu.”

Acewar Sakon, Kayayyakin da Sanatan ya raba sun hada da; Galan na manja, Buhunan shinkafa, kwalayen taliyar Noodles, tabarmi, barguna, da sauran kayan abinci na gida.

Tawagar da ta ziyarci karamar hukumar Kaura ta samu jagorancin Injiniya Namadi Musa wanda tsohon darakta janar na kungiyar addinai ta jihar Kaduna ne, tsohon shugaban karamar hukumar kajuru Honarabul Cafra Caino, shugaban karamar hukumar Jaba Honarabul Ben Jock. Honarabul Banta Bala Bantex, Honarabul Donatus Adamu, Honarabul Joy Akut da Saratu Abdulazeez.

A karamar hukumar Giwa, tawagar ta samu jagorancin Honarabul Bashir Zubairu Birnin Gwari, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna tare da mataimakin shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa Honarabul Nazir Sunusi, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad, Honarabul Ibrahim Shehu Haske da Alhaji Ibrahim Musa yayin da tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga shugaban karamar hukumar Giwa, Kungiyoyi, shugabannin al’umma da sauran Jami’an Jam’iyyar.

Hakazalika, a Karamar Hukumar Kaura, Tawagar ta samu tarbar Majalisar Gargajiya ta Kaura, Wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Kungiyar Cigaban Kaura da Kauran IDP Forum.

A karshe, Shugaban Mazabar Shiyyar Abubakar Rabi’u Abubakar, ya bayyana cewa tawagar ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da aka tanadar domin raba kayayyakin da su tare da jajanta musu bisa wannan abin takaici.

Leave a Reply