Sai Da Muka Yi Tafiyar Kilomita 3 A Kasa – Ya’u Abdullahi

0
505

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SHUGABAN Jam’iyyar APC a karamar hukumar Gada dake Jihar Sakkwato, arewacin tarayyar Najeriya Alhaji Ya’u Abdullahi, ya kasance daya daga cikin mutanen da suka tsallake Rijiya da baya lokacin harin da ‘yan Ta’adda suka kai wa Jirgin kasa da ya fito daga tashar Jirgin kasa ta Idu daga Abuja zuwa tashar Rigasa kaduna.

Da yake bayyana irin yadda lamarin ya faru kasancewarsa daya daga cikin mutanen da ke cikin Jirgin lokacin da lamarin ya faru a wani wuri idan an wuce kauyen da Alheri Kam yake kimanin mintuna 20 a kai ga tashar Jirgin kasa ta unguwar Rigasa Kaduna, sai kawai suka ji Jirgin da suke ciki ya fara tangal tangal zuwa can sai wani abu ya fashe nan take kuma suka fara jin harbe-harben Bindiga ta ko’ina, wato harbin kan mai uwa da wabi.

“Ina cikin taragon Jirgi mai lamba sha Bakwai nan da nan muka kwanta kasa a cikin taragon jirgin da muke ciki, bayan mun ji alamun abubuwa sun lafa, wato yan ta’addan sun ja da baya zuwa can bayan kimanin kamar awa biyu sai muka ji ana kwankwasa taragon da muke har muka gane cewa Sojoji ne sannan aka bude”.

Ya’u, ya ci gaba da cewa hakika “jami’an tsaron da suke tare da mu sun yi kokari domin sun mayar da wuta sai dai an fi karfinsu ne kawai, su ma sojojin da suka kawo mana dauki duk sun yi kokari kwarai domin sun yi aiki tare da nuna dabarun aiki wajen fito da jama’a daga ramin da suka fada sakamakon fargabar da suka shiga.

“Sojojin da suka kai dauki sun rika Goya jama’a ne a bayansu su na fitowa da su daga cikin rami wadansu kuma da ke da sauran karfinsu sun rika kamo gabar duwatsun da ke wurin suna yin tafiya kamar su na kan tsani domin su fito, sai kuma sojojin suka sanya mu a layi muka zazzauna bayan duk mun shiga layin sai suka tayar da mu tsaye muka shiga layi suka yi amfani da hasken wata mota kirar hilux, suka yi amfani da fitilar motar sai su ce wa jama’a ku tafi ga motarku can idan an kusa zuwa gare ta sai a kara gaba da ita motar a haka har sai da muka yi tafiyar a kalla kilomita uku a kasa, sannan muka Isa bakin kwalta inda aka ajiye motocin da za su dauke mu, an jera su a gefen titi haka aka dauko mu aka ajiye mu a dai- dai bakin kasuwa wajen labentis, isowa wurin sai muka tarar ya zama wata kasuwa ne duk da Dare ya yi, amma mutane na nan su na jiran mu iso wurin”.

“Kai akwai wata mata da take tare da wani mutum bayan an sanya mu cikin layi muna tafiya, ita ba ta iya tafiya sai wani soja a Karbe kayan da take rike da su a doka a bisa kanshi ya ce wa mutumin da suke tare ya rike mata hannu, ana nan muka yi ta tafiya har zuwa wurin motocin da aka ajiye za su dauko mu, kuma ni ne a sahun farko da muka shigo cikin jerin dogayen motocin da suka dauko mu”. Inji Ya’u Abdullahi.

“To Alhamdulillah, ni Allah ya tseratar da ni gani cikin koshin lafiya sai hamdala ta Allah kawai, amma ban ta ba shiga cikin tashin hankali irin wanda na shiga ba a wannan halin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here